Compiled by Princess Aysha Muhammad (Humaira)
π°π°π°π°π°π°
AUREN DOLE
π°π°π°π°π°π°
Story nd written by mufeeda Muazu
bismillahir rahamani raheem
Page 1 - 5
Kwance take a daki sai kuka take bata mai lallashinta tashi tayi ta dauko wayarta daga chargi tayi dialing number hello Aunty kinji abinda alhaji yace wai Dalhat xai aura mun kuma ni wlh bana sonsa hajiya dasu yaya duk sun goyi da bayansa
Don Allah kixo kiyi masa magana ko Allah yasa yaji maganarki ki taimakeni ki taimaki rayuwata na fashe da kuka daga can bangaren tace kiyi hakuri hudah ina nan xuwa insha Allah amma kin san alhaji magana daya yakeyi but i will try my best ke kuma ki cigaba da addua to aunty nagode katse wayar nayi
komawa nayi na kwanta na cigaba da kukana da dai naga kuka baxai fissheni ba na tashi na dauro alola naxo na tada sallah nai addua sosai sai wajen asuba bacci mai nauyi ya daukeni
Sai wajen karfe shidda da rabi na tashi na makara gashi gashi munada lectures karfe takwas idona duk sun kumbura wanka naje nayi tare da alola sallah nayi sannan na dauko wani atamfa green da orange nasa ba wani kwalliya nayi sosai ba
Falo nafito ban tarar da kowa ba kamar yadda na saba tare muke break duka harda su hajiya sannan masu xuwa makaranta su tafi masu xuwa wurin aiki su tafi yau na makara ba wanda yaxo ya kirani karasawa dining nayi tea rabin kofi na hada na kasa cin komai shima tea din da kyar na iya shanyewa nafi 15mins ina xaune ina tunani dafani da akayi shiyasa nayi firgigit dago Kaina nayi naga Ashe Jidda ce nace wai har kin shirya tace lallai nema hudah wai make damunki ne gashi idonki duk a kumbure alamar kinyi kuka kin gaji uhm abinda na iya cewa kije ki gaida hajia kixo mutafi kin cikani da tambaya kamar wata yar jarida
bari in dauko key kafin in dawo ki tabbatar kin gaisheta kin fito tare muka haye sama na shiga dakina ita kuma ta shiga dakin hajiya hand bag na dauka tare da makullin mota na fito a kasa na sameta nace muje ko a tare muka fito har farfajiyar gida naga ba motar Jidda
Aa Jidda ina motar taki ai ta lalace tana wurin gyara tun jiya Allah ya kyauta ameen ga key din ke xaki Jamu dama wlh bana jin dadi
Duk kin sa mun makara a tare muka shiga mai gadi ya bude gate muka hau titi sosai ba wanda ya karacewa dan uwansa kala har muka isa skull din munje mun tarar har ya shiga na kalleta nace Jidda yayaa xamuyi kennan kinga fa harya shiga dariya tayi
Au dariya ma kikeyi ko to aikene naga kin rude ba dole na rude ba kin sanfa halin lecturer nan mugu ne gashi yan mata suyita shige masa ko don sunga handsome gay ne
Ooo hudah kodai kema kina cikine Allah ya kyauta ni ai yayi mun yaro muna rafe muna hira har muka kai bakin class din ta kalleni na kalleta tace muyi addua kawai mu shiga haka kuwa akayi salam excuse us sir can we come in yace yes shiga mukay kowa sai kallon mu yake har muka xauna suna mamakin yadda akayi ya barmu muka shiga saboda kowa yasan kaidansa idan ya shiga ba mai shiga
cigaba yayi da lectures dinsa hankalina kwata kwata baya wurin jidda ce ta taboni ke lafiyarki kuwa ana karaku kin xauna kin buga tagumi gashi sir Haidar sai kallon mu yake a haka har ya gama ban tsinci komai ba a cikin karatun ba kallon mu yayi yace u d late comas follow me 2 my office ta kalleni na kalleta sannan muka ce okey sir
yana fita kobi ta Kansa bamuyi ba muka cigaba da harkokin mu Jidda ce ta kalleni tace wai ke hudah meke damunki ne rike hannunta nayi xo muje mota fitowa mukayi daga class wurin da mukayi parking din motar mu muka wuce shiga mukayi har kwallah ya taru a idona sharewa nayi nace Jidda wai baki San meke faruwa ba tace hudah kin sani a duhu dan Allah fada mun meke faruwa....
π±π±π±π±
muffy
π±π±π±π±
π°π°π°π°π°π°
AUREN DOLE
π°π°π°π°π°π°
Story nd written by mufeeda Muazu
bismillahir rahamani raheem
Page 6 - 10
Wani kwallar na dada sharewa Jidda dan Allah ki fahimce sosai kafin ki Yanke mun hukunci kuma kada ki dauka ko cin fuska ne aa ko daya alhaji xai mun auren dole narasa yadda xanyi kin san halin iyayen namu da tsatsauran raayi
Kuma ni kin san burina shine sai na gama karatu xanyi aure kuma ni koda xanyi aure to nafison in auri dan 35 and above bani son yaro wlh
Ta jinjina kai ta haka ne to yanxu wa alhaji ya xaba miki hawaye na xuba a ido na nace bakowa bane dan uwanki ne yaya Dalhat ba wai bana sonsa bane aa son da nike masa da ban ne wato so na yan uwantaka amma ni gsky bana jin xan iya rayuwa dashi a matsayin miji
na fahimceki Jiddah banga laifinki ba kuma banji haushinki ba ke kawatace ta wani gefen kuma yar uwa tun muna yara muke tare kin san sirrina kema na san naki kin san burina na San naki tayaya xan ki gsky saboda yaya Dalhat yana dan uwana nagode Jidda da kika fahimce
To yanxu tayaya xamu bullo ma wannan lamarin wlh Jidda kai na ya kulle na rasa yadda xanyi da rayuwata gashi gidan duk sun juya mun baya daga jiya xuwa yau ammah dai na kira aunty Khairat na Fada mata kin San alhaji yana jin maganarta ina fatan Allah ya dora mu a Kansa
Kawata gsky kina cikin matsala babba ko kin san yaya Dalhat din ma ba son auran yake ba jiya naji su ummi na cewa nan da wata uku kin san ance ya kawo mata amma yaki sai shekaran jiya ya kawo mana wata baki ganta ba yar duniya shine abbu ya koreta yace ko bayan ransa bai yarda ya aureta ba ana haka sai ga alhaji abbu yace yawwa alhaji mai xai hana a hada Dalhat da hudah kawai sai jin alhaji nayi yace ya bashi daki suka shiga shi kuma yaya Dalhat sai huci yake ya fita ban san me suka kara tattaunawa akai ba
Abinda yasa ban fada miki ba saboda bana son tayar miki da hankali shawarar da xan baki yanxu dai mubi komai a hankali share hawayen daya xubo mun nayi nace na shiga uku jidda yanxu katse mun karatu xaayi i don't know what 2 do jidda kiyi hakuri insha Allah xai barki ki cigaba take heart pls
Jidda nagode Allah ya bar kauna hudah let's go to d library fitowa mukayi daga mota mun fara tafiya kenan sai ga chairman din mu yaxo yace ina kuka shiga tun daxu inata nemanku kun sa anata bani wuya Jidda ce ta kalleshi tace toh fah meya faru yace sir Haidar ne yace duk inda kuke cikin skull din nan sai na nemo ku wai yace kuje kunki xuwa sai a lokacin na dago Kai nace to wai shi ina ruwansh damu oho xaixo ya takura mana
Hudah kuyi hkr dan Allah kuxo muje wurinsa ko na samu ya kyaleni da kyar na amince muka tafi har office din sir Haidar shi ya fara shiga muna baya yace sir gasu nan yace ok you can go ya tafi ya barmu wurin 5min ba wanda yayi magana gyaran murya yayi yace wato ku na kiraku but u refused 2 come jidda ce tace no sir yace what's are names Jidda ce tace my name is Jidda Aliyu yace Ashe ke daughter ce kefa nace hudah Sadiq yace nice names why do u come late 2day duk mukayi shiru yace am talking 2u Jidda ce tace we are sorry sir hudah ce bata da lpy dats why yace gidan ku daya ne ko kene bakinta tace aa hudah what's wrong sai a lokacin na dago ido na cike da hawaye na kasa magana fita daga office din nayi aguje sai mota kallon Jidda yayi yace lpy meya faru da ita saboda naga tunda tashigo class na idon a kumbure tace wani abu ke damunta and is a personal issue will solve it insha Allah
Yace nima xan tayaku da addua thanks alot malam yace can I get her phone no yea tabashi kije ki lallasheta
Tana fitowa wurin mota taxo don tasan ina can na nufa ta tarar dani sai kuka nake shigowa tayi tana ta lallashina da kyar nayi shiru ta jamu sai gida a kofar gidansu ta tsaya tace ni xan shiga gida inan shigowa anjima
To kawai nace na dawo maxaunin driver horn nayi mai gadi ya bude mun gate na shiga nayi parking cikin gida na wuce hajiya da yaya shahid a falo nace sannu da gida hajiya yawwa kawai tace xan wuce yaya shahid ya dakatar dani yace ke rashin kunyar taki har kai ki fice batareda kin gaida hajiya ba......
π±π±π±π±
muffy
π±π±π±π±
π°π°π°π°π°π°
AUREN DOLE
π°π°π°π°π°π°
Story nd written by mufeeda Muazu
bismillahir rahamani raheem
Page 11-15
Shiru nayi bance komai yace bada ke nake magana ba turo baki nayi saukar mari naji a fuskata kara na saki na duka a wurin yace ni kike turowa baki to aure ba fashi ko kina so koba kya so sai kin aure shi
Wani irin raxanenne ihu na saki na kwanta ina birgima a kasa ina cewa ni wlh bana so belt naga ya fara kwancewa tashi nayi a guje har ina watsar da jakana sama nayi ina gudu yana bina daki na shiga da karfi na bugo kofa nasa key
Kasa ya koma yace hajiya yarinyar nan sai an gyara mata xama wani tashen rashin kunya takeyi suna cikin magana Jidda ta shigo da salama ta tsuguna har kasa ta gaida hajiya da yaya shahid tashi tayi ta hawo sama dakina tashigo a kwance ta tarar dani ina kuka karasowa tayi tace subhanallahi meye haka kuma hudah ina ce kinyi shiru ashe har yanxu kina nan kina kuka
Ai sai ki jawo wa kanki wani ciwon xama nayi tare da share hawayena nace Jidda daga shigowata gidan da mari na fara cin karo yaya shahid ya mareni dukana yaso yayi aguje na gudo daki nasa key Jidda tace yaya shahid kuma nace shi mana wlh yaya shahid mugu ne tace haba hudah don Allah kidaina fadan haka harararta nayi nace kudai munafukai ne daga ke har shi naga taketakenku wlh gara ma karki soma don mugu ne Jidda tace kedai kika Sani da sharri
Jidda tace Kin ci abinci kuwa dan ni dai yunwa nakeji bari inje kitchen in dauko mana nace ni ba xanci ba na koshi tace Allah sai kin ci bari ki gani tashi tayi ta fita tana fita ni kuma na shiga toilet kasa ta sauka har lokacin su yaya shahid suna nan a falo hanyar kitchen tayi yaya shahid yace ba dai hudah xaki kaiwa abinci ba tace aa ta wuce tana shiga yana shigowa yaya shahid yace yawwa Jidda akwai maganar da nakeso muyi tace ina jinka yaya shahid yace bkm bane gsky ina sonki kuma da aure rufe ido tayi tsawon 3mins yace kinyi shiru amsarki nake jira....
Jidda tace yaya kadan bani kwana2 yaya shahid yace kai Jidda 2days baiyi yawa ba kuwa Jidda tace baiyi ba yaya
Yaya yanxu ya xanyi in koma sama yaya shahid yace Saboda me baxaki iya komawa ba Jidda tace kunyar hajiya xanji taga na shigo ka biyo ni ai sai tayi tunanin akwai wani abu a tsakanin mu yaya shahid yace aini nafison haka kinga sai a hada ayi bikin mu tare dasu hudah Jidda ta xaro ido tace yaya abi komai a hankali
Koda hudah ta fito daga wanka Jidda bata dawo ba har tayi sallah ta sauya kaya xuwa doguwar riga data dai shirun yayi yawa tashi tayi tace bari ta duba tagani ko lafiya tashi tayi a hankali cikin sanda take tafiya harta sauka falon shiru bakowa sai kawai ta wuce kitchen kai state
Ta bude kofar Jidda ta gani tsaye rike da kula a hannunta Hudah tace lallai ne Jidda saboda wulakanci daga cewa xakije kitchen shine kika xauna har nayi wanka na shiya hala dai sabon girki kikayi ne Jidda dai batace komai ba Hudah tace an magana kinyi shiru kamar wata... bata karasa taji ta taka wani abu juyawar da xatayi sai ganin yaya shahid tayi a tsaye aguje ta bar kitchen din sai daki harda sa key Jidda ta kalli yaya shahid tace yaya mai yasa Hudah ta gudu daga ganinka alhalin da ba haka kuke ba
Yaya shahid yace will talk later yanxu dai kije kuci abinci fita yayi ta kofar baya jidda kuma ta fito ba kowa a kasa sama ta haye ta murda kofar tajita a rufe ta buga taji shiru data gaji daga murya tayi tace ke dallah malama kixo ki bude mun kofa matsoraciya kawai....
Saida ta tabbatar Jidda ce sannan ta tashi ta bude kofar Jidda tace dallah bani wuri in wuce kan table ta dora kalar ta xauna a sofa Hudah kuma ta xauna a gefen gado.....
π±π±π±π±
muffy
π±π±π±π±
π°π°π°π°π°π°
AUREN DOLE
π°π°π°π°π°π°
Story nd written by mufeeda Muazu
bismillahir rahamani raheem
Page 16-20
Dedicated dis page 2 cwt sis Adama musa I love u so much
Hudah tace lallai Jidda wato soyayya kuke da yaya shahid ko Jidda tace da soyayya muke ai kece mutum ta farko da xaki fara san ai hudah tace to me naxo na ganku a kitchen kukeyi in ba soyayya Jidda tace dadina dake kin cika wutar ciki ki bari mu gama cin abinci xakiji komai
Hudah tace to shikenan ai ta janyo kular abinci tace ai saiki sauko muci ko tare suka ci abinci har suka gama
bangaren sir haidar tunda yaje gida yake tunanin Hudah gsky yarinyar ta tafi masa da hankali bai taba jin son wata yarinya haka ba daga ganinta sau daya Allah yasa dai tasoni kamar yadda nake sonta to wai meke damunta oho amma insha allahu xan tayata da addua haka yaita xancen xuci shi kadai
Suna gamawa hudah ta kalli Jidda tace oya ina jinki Jidda xatai magana
wayar hudah tayi kara alamar kira na shigowa ta duba taga bata san number din ba har ta katse Jidda tace waye hala yaya Dalhat ne shi yasa kika ki dagawa Hudah taxaro ido tace tab kina abu kamar baki san halin yaya Dalhat ba kila ma baida number ta Jidda ta bude baki xatayi magana kenan wayar ya fara kuka Jidda tace ki daga mana kiji ko waye mana
Daga wayar tayi shiru tayi daga can bangaren sallama akayi tace waalai kumus salam dawa nake magana yace ai kya bari a gaisa ko tace kaga malam in baka da abin Fada ni xan kashe wayata yace yi hkr kina magana da Haidar Aliyu daga bauchi daxu na amshi numberki wurin yar uwarki Jidda hope kin gane mai magana hudah tace eh sir haidar ko yace eh kiyi saving number xan kiraki anjima.....
Hudah ta aje wayar ta kalli Jidda tace ke kiba sir Haidar number ta tace eh shiya tambaya hudah tace shine kuma kika bashi bayan kin san halin da ake ciki Jidda tace to meye a ciki ki bada kai kawai Hudah tace lallai Jidda kina so ki sani a uku ko idan har na amince dashi xuciyata ta kamu da sonsa axo a rabamu me kike ganin xai faru Jidda tace ki cigaba da addua insha Allah komi xaiyi dai dai
Hudah tace uhm nidai fada mun mai ya hada ki da yaya shahid Jidda ta numfasa tace ina kitchen kawai sai gashi ya shigo wai shi yana sona kuma da aure....
Shine nace ya bani kwana2 inyi shawara Hudah tace toh ke kina sonsa ne Jidda tace kema ai kin san dole in so shi gashi kyakkyawa kwan2 dana ce ya bani jan ajine kawai Hudah tace lallai yarinya tayi xaben tumun dare gije ki aure shi wlh kirika shan duka
Hudah kema da abinda kikayi masa ba haka nan ba Hudah tace lallai ne wato yanxu kin fi sonsa ko Jidda tace ba haka bane kema kin san we are friends 4rever hudah tace uhm dadin baki ko murmushi Jidda tayi tace u will nt understand tashi tayi tace bari in shiga gida sai kin shigo ko kuma sai gobe tare suka fito daga daki har kasa hajiya ce xaune a falo tana kallo Jidda tace sai anjima hajiya
Ki gaida su hajiyar jidda tace to xasuji
Har waje hudah ta rakata Jidda ta shiga gida itama ta juya xata shiga gida taji ance ke tsaya waigawa tayi don ganin mai magana yaya Dalhat ta gani yana tawowa murguda masa baki tayi tace baxa a tsaya ba ta shige gida aguje.....
Karo tayi da yaya Aliyu rikota yayi yace ke anya lafiyarki Kalau kuwa dama ke nake nema naji abinda kikayi hakuri ta fara bashi saiga yaya Dalhat ya shigo yace Aliyu kaima rashin kunyar tayi maka hala Aliyu yace ai rashin kunyar ta ya girma hajiya tayiwa....
Yaya Dalhat yace lallai ka xaneta bari inje in dawo fita yayi yaya Aliyu ya fara janta ina tirjewa har falo bakowa sai yaya shahid nasan yau na shiga uku ba mai ceto na belt ya ciro dukanta yake tana kuka tana cewa wlh saidai a kasheni nace bana son shi yaya shahid yace kara mata Aliyu ke bakya ji ko yayay Aliyu yayita dukana har saida na kasa motsi.....
π±π±π±π±
muffy
π±π±π±π±
π°π°π°π°π°
AUREN DOLE
π°π°π°π°π°π°
Story nd written by mufeeda Muazu
bismillahir rahamani raheem
Page 21-25
Dedicated dis page 2 cwt sis Rabiatu Kebbi I love u so much
Sannan ya kyaleta tana kwance tana kuka a wurin yaya shahid ne daka mata tsawa yayi yace keep.....wa kikewa kuka a nan xaki tashi ko sai na kara miki da kyar ta iya tashi tana kuka harta isa dakinta a kasa ta kwanata tana kuka har aka kira sallar magriba tana kwance sai rawan sanyi takeyi gashi ta kasa tashi balle ta rufa har akai isha ba wanda ya ko leko yaga ko lpy bata fito taci abinci ba
Wurin karfe takwas da rabi sai ga Husna kwanwata ta bude kofa ganin ta a kwance a kasa yasa ta shigo Husna tace lpy Aunty Hudah kike kwance haka a kasa Hudah tace Husna taimake ni da ruwa mai xafi sosai a toilet Husna tace to ta tashi ta shiga toilet minti kadan ta hada mata ta fito tace Aunty Hudah ga ruwan nan idan kin gama yaya Dalhat na kiranki yana falo Hudah tace shida waye a falon Husna tace da yaya Aliyu girgixa kai kawai Hudah tayi tace kice masa nayi bacci Husna tace ai yaya Aliyu yace ko kina bacci a tasheki Hudah tace na shiga uku kice ganinan xuwa Husna tace to ta fita
Ita kuma Hudah da kyar ta tashi tashiga wanka sai da ta gargasa jikinta sannan tai alola ta fito doguwar riga tasa tai sallah mai ta shafa xumbulelen hijab tasa Sannan ta kwashi wayoyinta ta fito a falon sama taga su hajiya da alhaji hajiya dai bata ce komi ba alhaji ne yace sai yanxu kika daman fitowa tun daxu kin xaunar da mutum Saboda ba kya jin magana ko girgixa kai yayi yace kin tsireni da Ido wuce kiba mutane wuri kuma kije ki dawo ina jiranki
Tafiya take a hankali kamar kwai ya fashe mata a ciki har ta sauka kasa shi kadai ta gani a falon wuri ta samu can nesa dashi ta xauna batace dashi komi ba shine yace nine xan biyoki ko me kike nufi hararansa tayi tace fadi duk abinda kake so ka fada Kunne keji ai tashi yayi ya matso kusa da ita ya xauna xata tashi take hijabinta yayi tayi kaman xata fadi ta dawo ta xauna kallonsa tayi da jajayen idonta tace yaya wannan wani irin wulakanci ne so kake ka kaini kasa take yatsun kafarta yayi da takalmi sai da tayi kara hawaye na xuba a idon kasa magana tayi saboda axaba yace Ashe ke mara Kunyar karya ne. to bari kiji kamar yadda bakya sona to haka nima kuma rashin kunya ki cigaba karki fasa ni xan gyara miki xama thank god gasu Aliyu nan xasu tayani kafin ki shigo gidana
Kuka ne yaxo mata tace yaya Dalhat don Allah ka taimake ni kaje ka fadawa su alhaji baka son aure na ka fasa wlh bana sonka tashi tsaye yayi irin ko ajikin sa yace ni ina jin maganan iyayena kuma xanyi biyayya dabara ya rage gareki ko kiji magana ki xauna lafiya ko kiki ji ki sha wahala aure kuma aure ba fashi yana gama fadar haka yayi tafiyarsa ya barta nan dur kushe a kasa tana kuka dataga kukan baxai amfaneta da komi ba ta koma kujeta ta kwanta tana tunanin hawa sama bata san me alhaji xaice ba kilama dukanta xaiyi don tasan halin alhaji Dora hannu tayi akai tace ooo ni Hudahπͺ na shiga uku ba wanda aka taba yiwa auren dole a gidan sai ni gashi shima ba sona yake ba da karfi tace kai gaskiya ba xai yiwuba...
Lokacin da Hudah ta tafi wurin Dalhat alhaji yace hajiya yarinyar nan tunda akace xata auri Dalhat ta chanxa gabadaya kuma bashi xai hana auren ba ko xata mutu ne sai ta aureshi hajiya tace ni kaina abin na bani mamaki da anyi mata magana sai rashin kunya shi yasa na samata π daxu sai da Aliyu ya xaneta amma duk da haka kaga abinda tayi kafin ta fita alhaji yace hajiya mun yanke shawarar nan da sati daya xa ayi komi a daura aure nan da kwana 7 kowa ya huta ko me kika gani hajiya ya tambayeta
Hajiya tace yawwa hakan yayi na huta wlh......
π±π±π±π±
muffy
π±π±π±π±
π°π°π°π°π°
AUREN DOLE
π°π°π°π°π°π°
Story nd written by mufeeda Muazu
bismillahir rahamani raheem
Page 26-30
Hudah tagaji da xaman falo gashi tana jin bacci sosai given up kawai tayi ta fara tafiya a hankali harta kai sama cikin sanda ta murda kofar dakinta kenan alhaji ya daka mata tsawa yace ke..... me nace miki kafin ki fara shiru tayi ba tace komi ba wani tsawan ya karayi har sai da yan hanjin cikinta suka kada jikinta na rawa muryarta na rawa tace ka...ce in... Sameka a nan yace saboda ban isa bako
Kasa magana tayi saboda kukan daya xo mata hajiya tace to uwar kuka me akayi miki na kuka xakiwa mutane shiru ko kuwa hannu tasa ta toshe bakinta alhaji yayi gyaran murya yace ki bude kunnenki da kyau xaa daura aurenki da Dalhat nan da sati daya ko kinaso ko bakyaso tashi ki bani
mikewa tsaye tayi ta fara magana tana cewa dan Allah alhaji kayi hkr wlh bana sonsa ta rarrafa gurin hajiya tace hajiya don Allah kisa baki mana wlh bana sonsa kada kuyi mun auren dole alhaji ya taso da dori nan sa tashi tayi aguje ta shige daki ta rufe komawa yayi ya xauna yana kwafa
ASALINSU
Alhaji Abubakar. Sadeeq Aliyu da Alhaji Aliyu Dalhat haifaffun garin bauchi ne tare suka taso tun suna yara barci kawai ke rabasu makarantar primary daya sukayi secondry ma haka da sukaxo Jami a ne kowa basu sami admission a university daya ba yayinda shi alhaji Aliyu ya samu law a A.b.u xaria shi kuma alhaji Sadeeq ya samu Atbu bauchi yana karanta medicine ya kasan ce sunyi nesa da juna sai da a waya ko in dayan cikin ya samu time ya kaiwa dan uwansa xiyara ana nan wata rana Sadeeq ya kaiwa Aliyu xiyara suna xaune suna hira saiga wasu yan mata su biyu sun tafiya cikin skull Sadeeq ya kalli Aliyu yace abokina kaga abinda nagani kuwa Aliyu yace na gani yanxu yaya xa ayi Sadeeq yace muje mu same su kawai don gsky baxan iya hakuri ba tashi sukayi a lokacin har sunyi nisa sauri sukayi suka cin musu sallama suka farayi musu dayar tace ta amsa Sadeeq ne yace don in ba damuwa muna son magana daku suka ce don Allah kuyi hakuri sauri mukeyi Aliyu yace don Allah kuyi hakuri ku saurare mu koda na minti biyu ne xuwa uku da kyar suka tsaya suka sauraresu wuri suka samu suka xaxxauna
Aliyu ne ya fara magana yace muna xaune nida abokina muka ganku kunxo wu cewa so sai mukaga duk irin choise dimune da farko suna na Aliyu abokina kuma Sadeeq mu yan asalin jihar bauchi ne krat2 ne ya kawoni xaria ina fuculty of law ina final yr shi kuma abokina yana Atbu ya karanta medicine gsky mun gani muna so kuma da aure ni ina son choculate shi kuma yana son baturiya ne dukkansu saida sukayi dariya....
Sadeeq ya kara murmusawa yace duk abinda abokina ya Fada gsky ne yanxu Ku muke saurare muji ta bakinku farar ce ta numfasa tace duk munji bukatunku but muna so Ku bamu lokaci don muyi naxari Sadeeq yace hakan ma nada kyau but muna da bukatar Sanin sunayenku
Farar ce ta kara magana tace ni sunana Jidda othman ni yar garin kaduna ne kawata kuma sunanta Asmau Omar faruq yar asalin bauchi ammah suna kaduna da xama tare da iyayenta muna karanta micro biology 300l wow what a nice course exchanging phone number....
A haka suka rabu kowa na farin ciki
Jidda ta kalli Asmau tace kai gayun nan sun hadau Asmau tace ba kadan ba nace su bamu time ne kawai saboda muja aji Jidda tace ai nagane kawas...
A bangaren su Sadeeq kuwa murna suke sun sami matan aure gasu kawayen juna kamar yadda suke abokan juna Aliyu yace pls Kana xuwa gida ka fadawa su alhaji mun Sami matan aure...
π±π±π±π±
muffy
π±π±π±π±
π°π°π°π°π°
AUREN DOLE
π°π°π°π°π°π°
Story nd written by mufeeda Muazu
bismillahir rahamani raheem
Page 31 - 35
Sadeeq yace insha Allah Aliyu ya rakashi tasha ya hau mota sai Bauchi
Sadeeq na isa gida wayarsa ya ciro number Jidda yayi dialing kira daya ana biyu ta dauka sallama yace haba Jidda kya kira kiji yana koma gida ai tace lah wai har koma yace Yanxu na sauka shine nace bari in kiraki inji muryarki nd gsky da gske muke ba wasa Jidda tace to gdy nake
Haka soyayya ta kullu tsakanin su har iyaye suka shiga ciki a shekarar da suka gama skull suka sami aiki iyayensu suna mamaki irin abokan takarsu da sun so gina gida daya kowa da part dinsa iyayensu suka ce aa suyi dai kusa da juna saboda halin rayuwa da kuma shaani na mata haka kuwa akayi gidansu kusa da juna rana daya akayi bikinsu
bayan shekara daya Allah ya axurta Aliyu da samun da namiji wanda akasa suna Dalhat wato sunan mahaifinsa sunyi murna sosai
Aliyu Allah bai samu haihuwa ba har lokacin don haka kullum Dalhat yana wurin Aunty Jidda sai da Dalhat ya shekara uku Sannan jidda ta samu ciki murna wurin Sadeeq ko baa cewa komi itama asmau tana da wani cikin tare suka kara haihuwa Jidda ta haifi da namiji aka sa masa sunanan babanta wato othman suna kiransa da shahid ita kuma asmau mace ta haifa mufeeda haka rayuwa ta cigaba da tafiya
Jidda ta Haifa yara shida shahid khairat Aliyu jadeed Hudah sai auta asmau
Ita kuma asmau ta haifi yara bakwai Dalhat mufeeda Haidar hanifa Ryhan julaibib sai auta Jidda
cigaban labari
Koda hudah ta shiga daki babu abinda take sai kuka har dai ta gaji tayi shiru dan Kanta
Safe 8.30pm
Hudah ce ta fito daga dakinta cikin sanda harta sauka kasa bata ga kowa a falon ba dan haka cikin sauri ta nufi kofar fita harta bude taji ance ke ina xaki ba sai ta waigo ba yaya Aliyu ne fita tayi a guje ya bita harta kusa gate sai ga aunty Khairat da yaya jadeed yaya Aliyu yace riketa jadeed guduwa xatayi sai jin alhaji mukayi yace kai jadeed saketa ta tafi gidan uban da xataje yaya jadeed ya sakeni aiko yana sakinta ta falle ta fita daga gidan tasa kafa kenan taji an rikota ta baya ihu take kaman ranta xai fita tana cewa dan Allah yaya shahid ka sakeni babu inda xani wurin Jidda xani sai kuka take janta yakeyi har cikin gida..
Kowa na falo yaya shahid ya tangwarar dani a kasa a tsakiyar falo yaya dady cikin fushi ya daga bulala ya fara xuba mun ina kuka ina ihu duk inda nayi su yaya shahid su taroni....
Ana cikin haka Jidda tashigo aiko da gudu ta koma gida ta fadawa su Abbu da ummi a tare suka fito suka shigo da kyar Abbu ya kwace ni da gudu na koma bayan ummi na buya..
Abbu ya farawa alhaji Fada haba alhaji wanna wani irin duka ne haka kaman kana dukan barawo komai tayi ai kamata yayi ka bita a hankali yarinya ce karama alhaji yace kaman Hudah ne xan rika fada tana fada abin ma girma yayi yau an wayi gari xata gudu hudah na bayan ummi tace wlh ba guduwa xanyi ba wurin Jidda xani....
Alhaji yace kagani ko abbu yace yi hkr alhaji kowa ya xauna hudah dai tana gefen ummi sai shassheka takeyi....
Abbu ya fara magana kamar yadda kowa ya Sani ansa ranar auren Dalhat da hudah wata uku yanxu an komar dashi rana ita yau wato ranar asabar mai xuwa Dalhat dake xaune kai a duke dago yace alhaji ina neman alfarma dan Allah a bari in dan gama shirye shirye alhaji yace baka da wani damuwa duk wani shiri mun Riga mun gama shi.....
Hudah dake gefe sai kuka take ta tashi taje kusa da Khairat tace Aunty Khairat don Allah kisa baki mana a bari sai na gama krt2 Aunty Khairat tace kiyi hkr hudah kiyi biyayya
Ummi ce ta taso ta kama hannunta tace yi shiru ki share hawayenki tashi kije daki ki kwanta ki huta kinji Jidda rakata daki saida taga sun wuce ta juyo ta kalli hajiya tace don Allah hajiya ku kyale yarinyar nan ta hut a haka nan....
π±π±π±π±
muffy
π±π±π±π±
π°π°π°π°π°π°
AUREN DOLE
π°π°π°π°π°π°
Story nd written by mufeeda Muazu
bismillahir rahamani raheem
Page 36 - 40
Hajiya tace yarinyar nan bata ji su alhaji sunyi mun dai dai da suka dawo da daurin auren kusa kowa ya huta taje can tayi masa taurin kan ya chasata wlh ummi tace ina nan ba wanda xai taba mun ya hajiya tace masu ya kuje can Ku karata
su hudah na shiga daki hudah ta kalli Jidda a lokacin hawayen ma sun kafe sai kukan xuci tace Jidda kinji abin da su alhaji suka ce ko wai nan da one week ni yanxu yaya xanyi da wannan tsatsauran hukuncin sai kace su auren dole akayi musu yanxu Jidda meye shawara
Jidda ta numfasa tace shawara daya ne hudah hakuri kawai itace mafita tunda dai sun dage abin sai dai addua kawai amma da kika fito ina xaki har akace guduwa xakiyi akai miki irin dukan nan kaman an kama barawo
Hudah tace wlh jidda sharri ne kawai irin na ya Aliyu Jidda tace maiyasa kike sanda a lokacin da xaki fita hudah tace ina tsoron kada inga su yaya Aliyu a falo shiyasa ammah wlh wurinki xanxo Jidda tace to Allah ya kyauta hudah tace ameen
Dakin yayi shiru kowa da abinda yake sakawa a ransa wayar hudah ne ya katse musu tunani da kuka har ya katse bata dauka ba wani kiran ne ya kuma shigowa a kasalance ta daga wayar taga ashe sir Haidar ne karawa tayi a kunne cikin sanyin muraya tace hello sir Haidar yace haba hudah tun jiya nake kiranki baki daga ba yau ma saida ya kusa katsewa duk Nashiga damuwa Allah dai yasa lpy hudah tace lpy klu bana kusa ne sir Haidar yace amma ai kinga missed call ko hudah uhm bata ce komi ba sir Haidar yace nagane duk ajan aji neko to ykk hudah tace lpy klu har suka gama wayar hudah dai ga um sai uhm aje wayar tayi tare dayin tsaki tace hudah wannan mutumin yana son takurawa rayuwata Jidda tace tace tace wani mutumi kenan hudah tace wane kika San ban sir Haidar
Jidda tace mai yace miki ne hudah tace tatsuniyar gixo ai bata wuce ta koki Jidda tace ki dai bi komi a hankali ki kuma cigaba da addua
Hudah ta tashi tace bari in dan watsa ruwa ta shiga toilet Jidda kuwa kwanciya tayi tace bari tamike bada dade da kwanciya ba barci ya dauketa
A falo kuwa hajiya da ummi ne suke tsara yadda bikin xai kasance Dalhat ne ya shigo da leda a hannunsa katine ya tsuguna ya gaida iyayensa yace hajiya su Jidda na cikine hajiya tace eh ummi ce tace mai xakayi musu dan nasan halinka yace ummi ba wani abu xanyi musu ba kati xan basu in kuma tambayesu koda akwai abinda sake da bukata hajiya tace ke ummi ina ruwanki da abinda xaiyi musu kaji tashi kaje suna daki tashi yayi ya haye sama...
Jidda sai barcinta takeyi hankali kwance Dalhat ya turo kofar dakin dai dai fitowar hudah daga wanka kenan gashi daga ita sai towel iyakan shi cinya ko gwiwa bai kai ba kara tayi ko motsi ta kasayi shi kuma ya kafeta da ido ko kyaftawa bayayi
Karar tane ya farkar da Jidda daga barci bata kula da yaya Dalhat ba tace amma ke hudah baki da mutunchi mutum na barci ki tashe shi da kara haka xaki rika yiwa yaya ko hudah tai mata signal ido aiko tana kallon kofa hada ido sukayi da shi aiko ya sha mur yace wato Ku baku da kunya ko to tashi ki fita ki jira mu a falo ban ce ki sauka kasa ba sum sum ta mike ta fita.....
Tana fita hudah tai sauri ta janyo hijabinta ta saka shiko xama yayi a gefen gado yana murmushin mugunta hudah ko sai hararansa take tace malam ka tashi mun a gado don batare da kai akas siya ba murmushi yayi yace calm down saura kwana nawa ne a siya wani tare dani tsaki tayi aiko tasowa yayi yaxo har inda take tana matsawa yana matsawa har takai bango har suna shakar numfashin juna...
Take kafanta yayi ya murde mata baki...
π±π±π±π±
muffy
π±π±π±π±
AUREN DOLE
π°π°π°π°π°π°
Story nd written by mufeeda Muazu
bismillahir rahamani raheem
Page 41 - 45
Daga yau sai yau kada ki kuskura ki sake yimun tsaki if not yayi kwafa ita ko huda ba abinda take sai kuka gashi ya fasa mata baki tsawa ya daka mata sai da yan hanjin cikinta suka motsa
Wa kikewa kuka anan xaki tashi ko sai na lallasaki da sauri ta tashi tana goge hawaye gefen gado ya nuna mata ba musu ta xauna cikin shan mur ya fara magana
Dame da me kuke bukata na hidimar biki a tsiwace ta kalle shi da jajayen idonta tace bamu da bukatar komi daga gareka abu guda nikeda bukata a wurinka dan Allah ka taimaka ana daura auran ka sakeni ka bani takardata
Idan ba haka ba kai da xaman lpy har abada don wlh bana sonka na tsaneka Allah ko ganinka bana sonyi murmushin mugunta yayi sannan yace ashe ko xuciyarki xata buga don aurena dake ba saki duk da nidin ma ba sonki nake ba hukuri kawai xanyi biyayya
Saboda haka muxuba mugani ni dake aga wanda xai ci riba ya watso mata katin daya shigo dashi yayi ficewarsa
Yana fita ta kifa kanta a gado tana rera kuka a haka Jidda ta shigo ta sameta taga kati kuma a watse a kan gado dauka tayi ta karanta ya tabbata kenan saura one week
matsowa tayi kusa da hudah ta dafata hkr take ta bata akan tayi hakuri insha Allah wata rana sai labari dagowa tayi tace Jidda hakuri ya xama dole an dai riga an cuci rayuwata an hadani da wanda baya sona kuma nima bana sonsa gara shi namiji ne xai auri wanda yakeso ni kuwa fah wlh Allah sai ya saka mun Jidda tai sauri ta toshe mata baki tace kiyi hakuri kada kice haka iyayenmu baxa su taba xaba mana abinda bashi da kyau ba nasan abinda ciwo but don Allah ina so ki daure ki cije ki maida komi ba komi ba kin san dai ba fasawa xasuyi ba tunda sun kafe kisawa xuciyarki salama gara shi namiji
Hudah tace dan Allah kalli bakina fasa mun yayi fah saboda kawai yayi magana nayi tsaki tun yanxu ya fara xalunta mun inaga kuma na shiga gidan na xama nama kenan
Kema huta kin san yaya Dalhat baya son tsaki dan Allah hudah ki rika kiyaye abinda mutum bayaso ko don a xauna lpy but abinda yayi bai kyauta ba kiyi hakuri
Yanxu wani event kuka shirya mana keda angon naki ta tambaya cike da xolaya tsaki hudah tayi tace wlh Jidda ki kiyayeni tun da sauran girmanki a idona Jidda tai dariya tace tuba nake aunty amarya
Hudah dai bata kara cewa komai ba don ta kula Jidda neman fada takeyi..
A falon kasa kuwa hajiya da ummi su gama tattaunawa yadda bikin xai kasance xasuyi mothers day da kuma walima
Anan falon ya tarar dasu ya gaishe su xai wuce hajiya tace fatan dai komi lpy ko yace eh yana sosa keya ummi ko hararansa tayi da sauri ya bar falon ummi ma tashi tayi sukayi sallama da hajiya ta
A daki kuwa Jidda ce ta tattaro katinan da aka watsa a kan gado tace Hudah kinga katin kuwa wlh sun hadu yaushe xamu fara rabon katin harararta tayi tace rabon kati Allah ya kyauta ba wanda xan ba kati mayar masa dashi xanyi jidda ta mike tare da cewa kinfi karfina hudah tace meye haka ina xaki kuma jidda tace gida mana ta Fada tare da raba katin biyu ta dauki rabi ta aje rabi
Hudah tace jirani insa kaya muje ba musu ta koma ta xauna hudah ko drawer ta bude ta dauko wani material baki da ja tasa sannan ta saka bakin abaya mai ratsin ja ta dan murxa powder sai a lokacin ta tuna da wayarta akan dressing mirror wanda ta aje tun jiya da daddare....
Dauka tayi tare da dubawa 8missed calls da 2massages tana budewa taga duk number daya ne sir Haidar ne....
π±π±π±π±
muffy
π±π±π±π±
For comment 07065642314
π°π°π°π°π°
AUREN DOLE
π°π°π°π°π°π°
Story nd written by mufeeda Muazu
bismillahir rahamani raheem
Page 46 - 50
xama tayi a gefen jidda tace kinga Jidda tayani duba massages din nan ta amsa wayar tare da dubawa na farkon dai hakuri yake bada ko yayi wani laifi ne aka ki daga wayarsa dayan kuma na magiyace akan dan Allah tayi hakuri ta amshi soyayyar sa suna gama karanta a tare suka dago ido cikin ido hudah ce tayi karfin halin cewa Jidda na shiga uku yanxu ya xanyi
Jidda ta kalleta alamun tana son karin bayani hudah tace Allah jidda ina son sir Haidar tunda randa na fara sa shi a idona daurewa kawai nakeyi Saboda in tsira da mutunci na kada girma na ya xube gashi yanxu ya fito da bakinsa yace yana sona amma sai dai kash yaxo a kurarrar lokaci ya kike gani xaayi wayyo Allah Jidda na shiga uku
Jidda taja dogon numfashi ta dafa kafadunta tace kullum maganata dai daya ce nasan kida hakuri amma don Allah ki kira hakuri Kan wanda kikeyi ki cigaba da addua nima xan tayaki insha Allah komai xai wuce
Hudah wanda tuni hawaye ya gama wanke mata fuska ta rungumeta tace nagode sosai Allah ya bar kauna ya dada hada kanmu Jidda tace ameen ta goge mata hawayen tace yawwa koke fah da kina so ki bata kwalliyarki duk da nasan wannan gayun na yaya Dalhat ne ta fada cike da xolaya harara huda tabita dashi tare da kaimata duka da gudu Jidda ta fita tana dariya
Hudah ma tashi tayi ta dauki wayoyinta da sauran katin da Jidda ta bari ta saka cikin jakarta ta fito anan falon sama ta tarar da Jidda hararar ta tayi tace malama ai saiki tashi mu tafi ko tashi tayi tare dacewa wai ina xamu ne irin wannan wanka haka koda yake bai na tambaya ba koya kika ce hudah dai bata tanka ba dakin hajiya suka shiga bata dakin sai Husna jidda tace Husna ina hajiya take tace hajiya sun fita ita da alhaji hudah tace idan ta dawo kice muna gidan Abbu kada a nemi Husna tace a dawo lpy suka ce ameen
Suna fita farfajiyar gidan Hudah tace Jidda an gyara motarki kuwa Jidda tace eh waike ina xamuje ne hudah tace gidan aunty mufeeda da aunty Khairat nagaji ne da xaman wuri daya Jidda tace to shikenan
Suna shiga gidan Jidda ta wuce dakinta hudah kuma dakin ummi ta shiga suka gaisa Sannan ta fito ta shiga dakin Jidda ta Tarar ta shiga wanka ganin haka yasa tai sauri ta fiddo da I.v din daga jakarta da sauri ta fito ta nufi bq dakinsa ta kwankwasa har sau biyu taji shiru
Shiko yana can ya Fada duniyar tunani yana tuna yadda ya ganta ta fito wanka daga ita sai towel wanda ko cinyarta bai gama rufewaba gasu santala santala Ashe haka yarinyar take da shape gsky komi yaji shi yana mata kallon yarinya tai masa kankanta Ashe ta wuce tunaninsa uwa uba ga tsiwarta yana burgeshi tana magana cikin shagwaba kamar wata karamar yarinya yayi xurfi cikin tunani yaji bugun kofansa firgigit yayi ya tashi ya na mita waye xaixo ya dame shi mikewa yayi tare da xuwa ya bude aiko yana budewa idanunsa sukayi toxali da Hudah nan da nan ya daure fuska....
Ya fara magana ke lpy meya kawoki wurina ai kya bari a kawoki kafin ki kawo kanki har kin kosa nan da kwana bakwai dai wani irin bakin ciki yaxo mata wuya wani mugun kallo ta watsa masa tace Allah ya kyauta da aurenka da rashinsa duk daya ne a wurina don ni ban dauke ka a matsayin miji ba ka bari kashinka yai kwari saika kira kanka namiji bude baki yayi xai magana kenan tako watsa masa kitin tace ga tsiyarka nan
xaro belt yayi ganin haka yasa ta ruga a guje biyota yayi har falo taci saa kuwa ummi na falo da gudu ta buya a bayanta tana cewa ummi kin ganshi ko shiko gogan tsayawa yayi da belt a hannu yana muxurai
Yace dan Allah ummi ki matsa in xane yarinyar nan ummi tace lallai ka girma yanxu ka dubi tsabar idona kace in barka ka dakar mun ya Dalhat cikin fushi yace rashin Kunya fa take munfa .....
π±π±π±π±
muffy
π±π±π±π±
For comment 07065642314
AUREN DOLE
π°π°π°π°π°π°
Story nd written by mufeeda Muazu
bismillahir rahamani raheem
Page 51 - 55
Hudah tana daga bayan ummi tace Allah ummi ni ban tsokane shi ba kawai na daga ganina ya hau cewa wai na kawo kaina tun kafin a kawoni shine nace ai nan ma gidan mu ne ai shine fa ya biyoni da belt ta karshe maganar kamar xatayi kuka
Ummi ta kalleshi tace su yaya Dalhat anyi girman kawai kai bakaji kunya ba ko yau ta saba xuwa gidan ummi ko sai fada take masa Hudah tana bayan ummi tana masa gwaloπ a kufule yace ummi kina gani gwaloπfah take mun Allah ummi ki Fada mata ta bar tsokanata in ba haka ba tasan sauran ummi tace yo kai mahaukaci ne da xata tsokaneka fita mun a falo babban kawai kallon hudah yayi murguda masa baki tayi π kwafa yayi ya fita acikin ranshi yaji yarinyar ta kara burgeshi d way yadda take acting kamar yar drama
Yana fita ummi tace ai saiki sauko dodon naki ya tafi dariya hudah tayi tace Allah ya soni ummi da ba din keba yau da yaya Dalhat ya xaneni jiddah dake gefe tace haba dai wasa yake miki irinta masoya harararta hudah tayi tace ummi kin ganta ko ummi tace kunfi kusa ni kunga tafiyata tashi tayi xata shige daki hudah tai sauri tace ummi gidan aunty khairat da aunty mufeeda tace haba Ashe shiyasa a kayi kwalliya haka gashi kunyi anko eyee twince din ummi kunyi kyau naso ace rana daya xan aurar daku murmushi mukayi nace ummi Jidda ma ai ta fitar da miji kinsan waye Jidda tai sauri ta toshe mata baki
Ummi tace ke Jidda meye haka kikeyi jiddah tace Allah ummi karya take mun hudah tace ummi idan mun dawo xan Fada miki kuma ma kin sanshi ummi tace to hudah a dawo lpy ku gaishesu da kyau suka amsa da ameen ta shige daki tana murmushi
Hudah tace Jidda bari in dauko jakata a daki Jidda dake waje tace malama ga jakarki nan na dauko kina chan kina fama da surutu mutum yaita xuba kamar ruwan famfo hudah data fito tace eh din anyi bakinki ko nawa kuma sai na fada bari mu dawo Jidda ta mika mata jakarta gashi ni nagaji da riko hudah ta amshi jakarta mota suka shiga Jidda ce ta xauna wurin driver hudah kuma tana gefenta horn sukayi idi mai gadi ya bude musu gate
Suna fita titi Jidda ta dan kalli hudah tace ina xamu fara xuwa xatayi magana kenan wayar hudah ya fara ringing dago wayar tayi don ganin mai kirar ganin sunan yaya Dalhat tace hudah mun shiga uku yaya Dalhat ne ke kira hudah tace dauka mana kiji mai xaice parking tayi gefe guda ta daga wayar tace hello yaya magana ya fara cike da isa yace ina xaku duk inda kuke Ku dawo gida yanxu xatai magana ya katse wayar hudah tace lpy meyafaru Jidda tace wai yaya Dalhat yace duk inda muke mu dawo gida hudah tai tsaki mtsww dallah shareshi kawai in mun dawo ya kashemu Jidda tace gsky ina tsoron yaya Dalhat kinayi kamar baki san muguntar sa ba...
Hudah dai ta kafe sai sun tafi hakanan Jidda ta tada mota sai gidan aunty khairat sukayi horn mai gadi ya bude masu gate suna shiga parking sukayi direct cikin gidan suka shige a falo suka tarar da ita tasowa tayi tana faraa ta taresu tace maraba da amare hudah ta daure fuska tace haba aunty khairat ni bana so fah Jidda tace kinji aunty khairat kyaleta rigima takeji
Falo suka koma hudah ma ta kariso cikin falon ta xauna a one seater kawai sai ta fashe da kuka aunty khairat tace haba hudah har yanxu baki hakura ba kiyi hakuri don Allah kiyi hakuri kiyi biyayya wata rana sai lbr Jidda tace wlh hudah bata jin magana kullum haka nake fama da ita
Hudah ta dago da jajayen idonta tace ya kukeso inyi ne dan Allah kun San yadda nikeji ne xuciyata kamar ta fado kara ta saki tace wayyo Allah na shiga uku aunty khairat don Allah ki boyeni a nan....
masoya na ina muku fatan alkhairi Allah ya bar kauna
π±π±π±π±
muffy
π±π±π±π±
For comment 07065642314
π°
π°π°π°π°π°π°
AUREN DOLE
π°π°π°π°π°π°
Story nd written by mufeeda Muazu
bismillahir rahamani raheem
Page 56 - 60
Aunty Khairat tace ba dani ba ke wai kanki daya kuwa to wlh ki fita idona in rufe ni banga laifin yaya Dalhat first class ne wanda ko wacce mace take burin samu gashi ke kin samu amma kina wulakantawa hudah kuwa ko magana ta kasa banda hawaye ba abinda take banxa sukayi dani suka cigaba da hirarsu har Jidda take tambayar ina yara taga bata gansu ba Aunty Khairat tace suna hadda wayar hudah ce ta fara kuka tana neman agaji
ciro wayar tayi daga jaka numbern sir Haidar ne ya fito baro baro murmushi tayi ta daga wayar sallama tayi su Jidda kuwa duk sun xuba mata ido a bangaren sir Haidar amsa sallamar yayi tare da cewa ranki ya dade har kin sani cikin tunanin ko nayi wani laifin ne na kira har so ba adadi
nayi text nan ma shiru don Allah hudah ki tausaya mun wlh ina sonki so na gaskiya hudah ko murmushin dole tayi har saida hawaye suka xubo mata tana tausayinsu hello.....hello hudah kinyi shiru kina jina kuwa dogon numfashi taja a Sanyaye tace ina jinka time dinda ka kira wayar bata kusa dani ne kayi hakuri sir Haidar yace ah bkm to don Allah yaushe xan ganki don Allah karki ce aa pls ki taimakeni hudah tace to shikenan kaxo gobe in Allah ya kaimu by 4pm
Sir Haidar yayi godiya sukayi sallama Aunty Khairat tace dawa kike waya hudah tace wani course mate din mu xaixo ya kawo mana wani handout ne Jidda xatai magana hudah ta harareta Ashe aunty Khairat ta gani tace meye kuma na hararata saboda kin girbo karya bakiso ta fadi gsky ko to wlh ki fita idona in rufe inba haka ba su yaya shahida xan sa suyi maganinki hudah tayi narai narai da ido kamar xatayi kuka tace aunty alama nayi mata ta taso mutafi saboda har gidan Aunty mufeeda xamu aunty Khairat tace ai shikenan ku gaisheta da kyau
Tashi sukayi Jidda tace to aunty sai anjima duk suka rataya jakarsu aunty khairata tayo musu rakiya har inda sukai parking motarsu suna sallama sai ga babansu muftahulkhair wato mijin aunty kharat xuwa karisowa yayi da murmushi dauke a fuskarsa yace ah Jidda keda amarya ne a gidan namu gsky naji kamshi ya cika gidan ya fada cike da xolaya murmushi sukayi dukansu sannan suka gaisa motar su sukayi mai gadi ya wangale musu gate suka fice aunty Khairat da mijinta suka koma ciki
Suna fita kwalta suka hau sosai hudah tace Jidda kin san waye ya kirani daxu kuwa Jidda tace sai kin fada hudah tace sir Haidar ne wai don Allah yana so yaxo gidan mu shine nace yaxo gobe karfe hudu na yamma Jidda ta dan kalleta sannan ta maida hankali a tukin da takeyi
Sannan tace hudah Kanki daya kuwa kin San dai weekend ne kowa na gida bakya tunanin wani abu hudah tace abinda yasa nace yaxo tausayi ya bani kuma gsky ina sonsa dole in fada masa gsky baxan yaudareshi ba Jidda tace wannan gsky ne dai dai tai parking mota a farfajiya gidan aunty mufeeda
cikin falon suka shiga tare da sallama har sau uku shiru baa amsa ba kamshi ne ya bugi hancinsu alamun ana girki a kitchen ai da gudu suka shiga kitchen din aunty mufeeda na hada salad kawai sai ganinsu tayi kamar anjeho su aunty mufeeda tace wai mai yasa ku bakwa girma ne kullum haka kuke kamar wasu kanan yara ta kalli hudah tace harda ke amaryar yaya nan da nan ko ran huda ya baci duk wani annurin dake fuskarta ya kau ta shagwabe fuska kamar xatayi kuka tace Allah aunty bana son ana kirana da wannan sunan
Aunty mufeeda tace wai ke hudah meyasa bakya jin magana ne to wlh kiyi dai a hankali kunfi kowa sanin halin iyayen mu tunda suka furta to kome xakiyi ba fasawa xasuyi ba Aunty mufeeda ta dafa ta tace kiyi hakuri hudah insha Allah ba xaki tabe ba hudah ta share kwallar daya xubo mata batace komi ba jidda ce tai magana tace aunty kullum sai na Fada ma but taki ta kwantar da hankalinta aunty mufeeda tace to iyayen magana bari inxo gidan miji xaki fito dashi don banga ampanin xaman ba Jidda tace aunty skull dinfa aunty mufeeda ta tsaki ta juya ta cigaba ta aikinta hudah tace aunty inasu hibba aunty mufeeda tace sun fita da dadynsu juyowar da xasu kawai sai ganin yaya Dalhat sukayi a kofar kitchen fuskar nan babu annuri yayi shigar kanan kaya sun amshi jikinsa kai gsky Dalhat ya hadu ba karya
*waye Dalhat*
Dalhat matashin saurayi ne wanda shekarunsa basu wuce talatin da biyar ba kyakkyawa ne ajin farko dogone shi yanada haske ba sosai ba irin choculate din nane hanci dogo bakinsa dan daidai yayi law ya karanta yanxu haka ya gama PhD dinsa yana aiki a. A.b.u xaria lecturer ne a fuculty of law......
π±π±π±π±
muffy
π±π±π±π±
π°π°π°π°π°π°
AUREN DOLE
π°π°π°π°π°π°
Story nd written by mufeeda Muazu
bismillahir rahamani raheem
Page 61 - 66
Hudah na hada ido da Dalhat da gudu taje bayan Aunty mufeeda haka ma Jidda Aunty mufeeda tace ku lpynku klu kuwa Jidda ce ke nuna mata kofa kallon kofar tayi don taga me Jidda ke nuna mata yaya Dalhat tagani da dorina a hannunsa fuskar nan babu alamun wasa a cikinsa itama kanta sai data tsorata rufe kofar yayi ya fara takowa a hankali aunty mufeeda tace ina yini yaya
cikin daurewar fuska ya amsa da lpy klu tunda taga haka bata kara cewa komi ba magana ya farayi cikin isa mufeeda dake da Khairat Ku kuke goyawa yaran nan baya suke iskancin da sukaga dama ko aunty mufeeda xatayi magana ya katseta cikin tsawa yi mun shiru kallon Jidda yayi yace ke mena gaya miki cikin rawar murya da in ina tace hu...hudah ce ta...wani tsawan ya daka mata tace mene Jidda wanda tuni hawaye ya gama wanke mata fuska tace hudah ce tace a kyaleka kawai mu tafi kawai
Jidda tace don Allah yaya kayi mana hakuri baxamu kara ba yaya Dalhat yace kuxo nan hudah tayi karfin halin cewa baxa a xo ba wai kai ina ruwanka damu ne duk kabi ka takura ma rayuwa
Kara fusata yayi yace eh lallai ke mufeeda matsa kafin in hada dake aunty mufeeda ganin da gaske yakeyi yasa ta matsa su hudah kuwa suka fara neman hanyar guduwa amma ina ba hanya ya tufe kofar taku daya yayi ya rikosu da hannnu daya
hudah ce ta fara kokarin kwace wa amma ta kasa saboda irin rikon da yayi musu ba na wasa bane dukansu yakeyi ta koina da dorina sai kuka suke suna bashi hakuri ko sauraronsu baiyi ba saida yayi mai isarsa sannan ya kyalesu
Kallon mufeeda yayi dake gefe tana hawaye yace ke kuma lpy me akayi miki tai sauri ta share hawayen tace haba yaya irin wannan duka haka Saboda kawai sunxo gidana ai dai kayi musu hakuri harsu koma tsawa ya daka mata yace xakiyi mun shiru ko kuwa falo ta fita ta bashi wuri don tasan halinsa xai iya dukanta baxaiji kunyar dukanta ba
Su hadah na gefe sai kuka suke ido ya kada yayi jajir Dalhat yace kuyi mun shiru ku taso Ku wuce ba musu suka tashi falo suka fito aunty mufeeda na xaune ta xabga uban tagumi tana tunani irin xafin xuciya na Dalhat gsky tana tausayawa hudah
Dalhat yace mata mun tafi agaida yara da mai gidan in sun dawo a sanyaye ta amsa fita yayi jidda ta dau mayafinta ta fita hudah ce tai karfin halin yi mata sallama ta fito a tsaye yake ya jingina a jikin motarsa
motarsu suka nufa yana ganin haka ya karisa wurinsu ta baya basu san da xuwan mutum ba sai jin kawai sukayi anja musu mayafi xasuyi ihu sai sukaga yaya Dalhat ne shiru sukayi yana jansu har suka kai wurin da ya aje motarsa ya bude front seat ya jefa hudah ya rufe Jidda kuma ya jefata baya
Idon nan murtik kamar arne yayi layya har suka mika titi ba wanda yayi magana sun kusa gida wayar hudah ya fara ringing hannu tasa ta ciro wayar ganin number ne ba suna yasa bata daga ba har ya katse kira aka karayi still dai wannan numbern ne wani kallo ya watsa mata mai cike da tuhuma
Fige wayar yayi ya daga shiru yayi daga can bangaren kuwa Haidar ne yace hello sweet heart jin shiru yasa ya kara cewa hello kina jina kuwa Dalhat ya katse wayar cikin tsananin kishi wanda bai san yanada ita ba
Dai dai kofar gida horn yayi mai gadi ya bude masa gate ya shiga gidansu hudah yana yin parking ko waccensu ta murde kofa xata Rita sukajita gam a rufe
budewa Jidda yayi ta fita ita kuma hudah kin bude mata yayi kallonsa tayi cikin karfin hali tace ka bude mun xan shiga gida....
π±π±π±π±
muffy
π±π±π±π±
For comment 07065642314
π°π°π°π°π°π°
AUREN DOLE
π°π°π°π°π°π°
Story nd written by mufeeda Muazu
bismillahir rahamani raheem
Page 66 - 70
HIQAYA ONLINE WRITER'S ✍πΌ
Daure fuska yayi yace idan kuma naki fah kwallah ne ya xubo mata tasa hannu ta goge shiru ne ya biyo baya tsawon 3minute Dalhat ne ya katse shirun da cewa waye ya kiraki a waya yanxu hudah tai shiru ba tace kala ba har ya gaji da jiran amsa tsawa ya daka mata har saida ta firgita yace bada ke nakeyi ba cikin muryar kuka hudah tace ni ban san kowaye ba dada harxuka yayi idanunsa suka rune nan da nan jikinta ya fara rawa tace Allah yaya ban san kowaye ba
Dalhat ya buge bakinta da karfi hudah ta rike bakin tana kuka mai ban tausayi cikin rashin damuwa da kukanta ya fara magan da kakkausar murya xakiyiwa mutane shiru ko kuwa ni xaki rainawa hankali mutum ya kiraki a waya harda cewa swt hrt sannan kice baki sanshi ba to bari kiji wlh ki kiyayeni idan ko hmm kwafa ya bude kofar yace dallah fita mun a mota fitowa tayi rike da baki tana kuka harta juya xata wuce ta dawo tace masa mugu kawai Allah sai ya saka mun tayi wucewarta ciki Dalhat yana mota yana tunanin rashin kunya irin na hudah lallai akwai aiki don saina gyara mata xama ya Fada tare da yin reverse ya bar gidan
Hudah koda ta shiga parlour jidda da yaya shahid ta gani xaune da gani hakuri yake bata Allah sarki hudah baiwar Allah ba mai share mata hawaye wasu xafafan hawaye ne suka xubo mata xata wuce yaya shahid yace ke xo nan ba musu a hankali take tafiya harta je tace gani kallonta yayi sama da kasa har time din hawaye bai daina xuba a fuskarta ba
Yaya shahid yace kukan me kikeyi bayan duk abinda ya faru ke kikaja saboda rashin jin magana irin naki kina so ki koyawa Jidda hudah da ranta ya baci ta kalli Jidda tace ke kika fada masa haka yaya shahid ya katseta da cewa to mara Kunya ba ita ta fada mun ba nine na fahimci haka ki kiyaye niππΌ ya nunata sannan yace ta tashi ta bashi wuri
Hudah ta tashi jiki a Sanyaye ta nufi sama direct dakinta ta shiga ta rage kayan jikinta ta dauki wayarta ta koma gado tana kunnawa text ta fara gani da numbern da aka kirata cikin bude bude ga abinda yake cewa
Assalamu alaikum fatan gimbiyar tawa tana lpy daxu na kiraki so bana jinki sai na kashe hope everthing is fine urs Haidar hafeex
Hudah tai murmushi tace Allah sarki Ashe sir Haidar ne reply ta tura masa kamar haka
Waalai kumus salam lpy klu d time dat u call me I was busy driving thanks 4 caring
Ta tura masa sir Haidar na xaune shida hajiyarsa yaji karar text dauko wayar yayi don ganin sakon meye yana dubawa yaga Ashe gimbiyar tasa ce murmushi yayi ganin text din amsa ya bata kamar haka
thanks dear love u extend my greeting 2 sis Jidda
Shigowar text dinsa yayi daidai da shigowar Jidda dakin waigowa hudah tayi ta harari Jidda tace maiya shigo dake dakina ai kamata yayi ki bishi dakinsa sai yaci gaba da lallashinki a can in ga karshen soyayya mtsw....tayi tsaki ta koma ta bude text din da ya shigo murmushi tayi data gama karantawa Jidda dake gefe ta dada mata duka a baya tace yar iska dariyar me kikeyi ta fige wayar hudah tace malama kibani wayata tunda ba da yaya shahid aka siya mun ba Jidda tace baxaa bayar ba hudah bata kara cewa komi ba Jidda ta bude wayar ta dudduba duk text din saida ta duba
Tashi tayi daga inda take ta koma kusa da hudah dake kwance ta dafata bata dago ba Jidda ta leka taga Ashe kuka take mara sauti fuskarta duk hawaye Jidda ta goge mata fuska tace jiddah tace haba hudah don Allah kiyi hakuri man ki daina kukan nan haka nan hudah ta tashi ta xauna tace Jidda kenan hakuri dai hakuri kullum itace kalmar haba dubi irin wulakancin da yayi mana a gidan aunty mufeeda kaman mu da girman mu da komi yayi mana duka kamar wasu yayan sa duk dai saboda kina dayakeyi kenan baxa muyi xumunci ba
Kuma aike kinada wanda xai lallasheki ya baki hakuri kiji sanyi a ranki nikuwa fah ba mai kaunata sai kace wata mujiya tana kaiwa nan ta fashe da kuka Jidda ta rungumeta tana lallashinta har sai da tai shiru Jidda tace nima abin na damuna sai dai ba yadda xamuyi tunda anfi karfin mu Hudah taja dogon numfashi tace Jidda Allah idan aka cigaba da matsa mun xan bawa kowa mamaki Jidda tace aa hudah kada kije ki aikata abinda nan gaba xaki kuka dashi muyi hakuri mu cigaba da addua insha Allah komi xai xama tarihi.....
π±π±π±π±
muffy
π±π±π±π±
For comment 07065642314
π°π°π°π°π°π°
AUREN DOLE
π°π°π°π°π°π°
Story nd written by mufeeda Muazu
bismillahir rahamani raheem
Page 71 - 75
HIQAYA ONLINE WRITER'S ✍πΌ
Hudah tace jidda abin yayi yawa ta ko ina ba sauki Jidda tace hakane addua itace kawai mata hudah tace to Allah yasa mudace Jidda ta amsa da ameen hudah tace yawwa Jidda kinga text ko Jidda tace eh na gani ammah ai number ne waye hudah tace sir Haidar ne Ashe shine ya kira mota shine yaya Dalhat harda duka na Saboda nace ban san number din ba muryar namiji yaji Ashe Jidda tai dariya harda shewa tace Allah hudah ki yarda dani yaya yana sonki hudah ta harareta tace karya kike dayana sona koda bana sonsa lallashina xai rikayi ba ya rika sani kuka ba Jidda tace irin tashi salon soyayyar ne haka hudah tace salon soyayyar mugunta ba Jidda tai dariya tace baxaki gane ba kila sai xuwa nan gaba so back to business yanxu ya kike so ayi hudah tace so nake ki tura masa da address din gidan nan gobe xaixo jidda ta dafe kirji ta xaro ido π³ ke hudah yaxo yayi miki mene hudah tace ke dadina dake tsoro kamar farar kura to bayani kawai xanyi masa mu bawa juna hakuri
Jidda tace mai xai hana idan mun hadu a skull sai kuyi duk maganar da xakuyi hudah tace aa gara dai yaxo kuma ya rokeni don Allah in bashi dama yaxo gidan mu jidda tace hudah rashin jin maganarki da kafiyar ki ke Janyo mana Fada wata rana harda duka haba hudah tace yi hakuri Jidda daga wannan ai shikenan Jidda tace ya xanyi dake bani wayar hudah ta dauki wayar ta mika mata Jidda ta rubuta address ta tura masa tace gashi nan na tura masa ni bari in shiga gida wurin ummi hudah tace ki cewa ummi tayi hakuri ban shigo nabata labarin ba kamar yadda nace ina tsoron haduwa da yaya Dalhat ne Jidda tayi mata gwalo π tace gara ai da so kike ki tona mana asiri ko ta fadi haka tare da fita daga dakin hudah ma tashi tayi tabi bayanta suka sauka falon kasa hajiya ce a falon tana kallo Jidda tai mata said a safe ta fita hudah kuma ta rakata waje sukai sallama ta shigo gida ita kuma ta wuce gida
Jidda na shiga harabar gidan su taga motarta tayi mamaki kwarai don a iya saninta a gidan Aunty mufeeda suka bar motar Ashe bayan da ya sauke su ya koma ne ya dauko motar koda ta shiga cikin gidan ummi bata falo don haka direct dakin ummi ta shiga ta tarar da ita a gefen tana xauna tana waya Jidda ta samu wuri ta xauna har sai data gama wayar tace ummi mun dawo ummi tace to sannunku da dawowa ya naga idonki yayi ja kuma jikinki duk shedar bulala Jidda ta dukar da kai tace bkm ummi ta daka mata tsawa tace xaki Fada mun wanda ya dakeki ko sai na kara miki da nawa cikin rawar murya Jidda tace yaya Dalhat ne yabi mu gidan Aunty mufeeda yayi mana duka nida hudah ran ummi ya baci sosai tace mai kuka yi masa Jidda tace bkm wai meyasa muka fita ummi ta dauki waya ta kirashi tace duk abinda yakeyi ya bari yaxo tana nemansa dama ba nisa yayi ba yana waje ya shigo a rude ganin ummi ranta a bace ga kuma jidda a kasa ta dukar da kai sai da gabansa ya fadi yace ummi gani
Ummi tace na baka 2mins kira mun jidda Kuxo tare yace to sannan ya fita hudah kuwa bayan ta dawo daga rakiyar Jidda a falo ta xauna wurin hajiya tace hajiya don Allah ki saka baki a daga auren nan wlh ban shirya ba hajiya tace lallai wuyanki yayi kauri to ai sai kije ki samu su alhaji suda suka yanke hukunci amma bani ba hudah taja bakinta tai shiru sai hawaye dayake ambaliya hajiya tana kula da ita tana kuma tausaya mata amma dole ta nuna mata su suka haifeta ba ita ta haife su ba
Kowa yayi shiru hajiya ta maida hankalinta ga kallon da takeyi ita kuma hudah tana nata sanaar wato kuka Dalhat ya shigo da sallama hajiya amsa hudah ta tashi hajiya tace dawo ki xauna ina kuma xaki hajiya xata tashi Dalhat yace kiyi xamanki ummi ce dama take neman hudah tace muxo tare....
π±π±π±π±
muffy
π±π±π±π±
For comment 07065642314
π°π°π°π°π°π°
AUREN DOLE
π°π°π°π°π°π°
Story nd written by mufeeda Muazu
bismillahir rahamani raheem
Page 76 - 80
HIQAYA ONLINE WRITER'S ✍πΌ
Hudah ta balla masa harara tace hajiya karya yakeyi ummi baxa tace muxo tare ba hajiya tace xaki rufe ma mutane baki ko sai na fasa shi mara kunya kawai waye xaiyi miki karya hudah tai shiru bata kara cewa komai ba tana xaune ko motsawa batayi ba kuma bada niyyar tashi hajiya tace kefa yake jira hudah tace hajiya Allah dukana xaiyi idanunta suka kawo kwallah shi kuma duk sai yaji kunya ya dukar da kai hajiya tace ko yanka ki xaiyi sai kinje ba yadda ta iya dole ta dauki mayafinta yana gaba tana biye dashi suna fita ya juyo ya kalleta yace kawo hannunki harararsa tayi tace indai saika rike hannuna ne sai dai a fasa don ni ba yar isaka bace irinka matsowa yayi daf da ita yace nine dan iska ko lallai xanyi maganinki saura kwana nawa ne yace bari kuma na fada miki kika kuskura kika fadawa ummi na bigeku wlh ranki sai ya baci don haka ki kula da kalamanki cikin jin haushi da kalamansa tace sai dai ka kasheni said na fada Dalhat yace muxu ba mugani yayi gaba abinsa hudah na biye shi a baya har suka shiga gidan a falo suka tarar da ummi da Jidda
Hudah ta samu gefe kusa da Jidda ta xauna tace ummi gani ummi ta kalleta dakyau tace hudah meya samu idonki yayi ja haka Dalhat gabansa ya fadi yana adduar kada hudah ta tona masa asiri hudah tace ciwo yakeyi ummi cikin fada ummi tace hudah yaushe kika fara karya idan idonki na ciwo wannan shedanfa xaki fada mun gasky ko sai na kara miki hudah da tuni hawaye ya wanke mata fuska tace yaya Dalhat ne ya dake mu a gidan aunty mufeeda ran ummi ya baci ta wanke shi da mari har sau biyu ji kake tasss......ummi tace gasu nan ka kashesu nace inga gawarsu tunda har xakayi musu irin wannan duka kaman ka samu jakuna to wlh ka fita daga idon in rufe Dalhat kuwa sai hakuri yake bata ga xafin mari daga karshe tace lallashe mu sannan kuma tace ya raka hudah gida kuma wlh idan ya tabata ranshi sai ya baci ba yadda ya iya hakanan ya rakata bai kulata ba har suka shiga gidan lokacin ana kiran sallar issha saboda haka yana fitowa masallaci
Hudah kuma dakin hajiya ta shiga ta tarar da tana sallah fitowa tayi ta tafi dakinta don yin sallah koda ta idar tai wanka ta rage kayanta wayarta ta dauko ta Kunnu tana game Husna ce ta shigo dakin tace Aunty hudah hajiya na kiranki hudah tace tana ina ne Husna tace tana dakinta a tare suka fito Husna ta xauna a falo hudah ta shiga dakin hajiya tace hajiya gani hajiya tace to ai naganki miko min kofin can na kan dressing mirror hudah ta dauko ta mika mata hajiya tace magani ne ki shanye yanxu ki bani Kofin hudah ta ya mutsa fuska tace hajiya ni lafiyata klu baxan sha ba hajiya ta daka mata tsawa nan da nan ta shanye ta mika mata Kofin xan tashi ta harareni ta koma ta xauna hajiya ta dauko wani magani ta hada da madara peak ta hadah ta mika mata ta shanye tana bata rai hajiya ta dauko wani turare a kwalba tace wannan a ruwan wanka xaki xuba safe da dare kuma wlh idan kika aje sai ranki ya baci
Tashi ki bani wuri harta tashi hajiya tace kinyi wanka ne hudah tace eh hajiya tace shikenan saiki fara amfani dashi gobe hudah tace to hajiya hudah ta fita jiki ba kwari yaxaayi a rika bata irin wannan abun bayan ita ba auren soyayya ba a dakeka a hanaka kuka a falo ta tarar da Husna tana kallo hudah tace Husna dan aje mun turaren a dakina Kan dressing mirror
π±π±π±π±
muffy
π±π±π±π±
For comment 07065642314
π°π°π°π°π°
Auren Dole
π°π°π°π°π°
Bismillahir rahamanir raheem
Story And
Written
by
mufeeda Muazu
Page 81,, 85
HIQAYA ONLINE. WRITERS ✍πΌ
Hudah na xaune a falo tunani kala kala a cikin ranta hajiya ta fito daga daki ta kalli yaran nata guda biyu tace lpy naga kunyi jugum kowa ta tsira ma tv ido kunci abinci kuwa Husna tace aa dama muna jiranku ne hajiya tace ai sai ku taso ga alhaji nan ma ya dawo ku taso muje dining suka nufa a can suka tarar da su yaya shaheed da alhaji Husna tayi saving din kowa san nan tasa nata abinci suke ci ba mai magana sai karan chokula kawai kakeji Husna ce tace alhaji dama kawai a hada auren Aunty hudah dana yaya shahid alhaji yace Allah ko auta to ai yayan naku bai kawo mata ba Husna tai sauri tace yanada budurwa ni na Santa shahid da ya tsaya kallon Husna yana harararta tunda ta fara magana ita bata San ma yanayi ba ya daka mata tsawa yace ke kiyiwa mutane shiru mara kunya kawai kema auran xaayi miki kowa ya huta π Husna ta shagwabe fuska kaman xatayi kuka tace alhaji kagan shiko alhaji yace kyaleshi auta ba wanda xai miki aure yanxu kinji Fada mun waye budurwan shashid yaja kujera xai tashi alhaji yace ya koma ya xauna ba yadda ya iya hakanan ya koma ya xauna Husna tace Jidda ce ta gidan ummi shahid dukar da kai yayi ji yake kaman ya nutse saboda kunya
Hajiya da alhaji sunyi
Farin ciki da jin haka hudah tana xaune kaman hoto batace komi ba alhaji yace Husna ngd da wannan Albishir naki alhaji ya juyo wurin shahid yace shine tuntuni kuka boye mana shahid dai bai ce komi ba hajiya tasa albarka alhaji yace ranar daura aure sai asa rana hajiya tace hakan yayi har suka gama hudah bata tanka ba haka kuma ba wanda yabi ta Kanta tashi tayi ta tafi dakinta falo suka koma sun danyi hira kadan kowa ya tashi falo ya rage daga alhaji sai hajiya Husna tana dogon kujera tana barci alhaji yace hajiya bawai naga kuna ta shirye shirye ba walima kawai xaayi Don bamu son bidiar nan hajiya tace to alhaji yadda kace haka xaayi
A bangaren Dalhat kuwa tunda ya fita bai koma gidan ba saboda bacin rai wai akan ya daki su hudah ne ummi ta mareshi a gabansu saboda su raina shi gidan wani abokinsa ya tafi a can yaci abinci suka sha hira sai wurin tara ya tashi sukayi sallama ya rako shi har wurin motarsa sai da ya shiga mota yaga kati shi kwata kwata ya manta dashi sauri yayi ya ciro ya mika mata abokin yace Ahmad gashi don Allah kada kace komi abin ne yaxo cikin gaggawa don Allah kaba wa sauran ni gobe xan koma Ahmad ya am tare da cewa wacece wannan mai saar Dalhat yayi murmushi yace ai kasanta hudah ce Ahmad yace gaskiya kayi Saar mata Allah ya Sanya alkhairi Dalhat ya amsa da Ameen sukayi sallama ya tafi Dalhat na shiga gida part dinsa ya wuce yayi shirin barci
Asubah tagari
5.30am hudah ta tashi tai sallah tunda tai sallah bata koma ba tayi axkar ta dauko Qur ani tayita karatu har gari yayi haske Sannan tayi addua ta gyara dakinta tsar Sannan ta shiga wanka harta shiga ta tuna da turaren da hajiya ta bata fitowa tayi ta dauka ta xuba a ruwa take toilet din ya gauraye da kamshi tai wankanta ta gama harta shirya bata daina kamshin ba kai wannan turare da kamshi yake ta Fada a xuciyarta kwalliya tayi sosai wanda rabonta da irin shi tun kan ace xata auri Dalhat
Ta fito fuskarta cike da walwala da farin ciki a corido ta hadu da hajiya hudah tace lah hajiya wurinki xanxo ina kwana hajiya ta amsa tace hudah kinyi kyau ga kamshi hudah tayi murmushi tace ngd hajiya
π±π±π±π±
muffy
π±π±π±π±
For comment 07065642314
π°π°π°π°
Auren Dole
π°π°π°π°π°
*Bismillahir rahamanir raheem
Story And
Written
by
mufeeda Muazu
Page 86 - 90
HIQAYA ONLINE. WRITERS✍πΌ*
dining suka wuce suna xuwa hudah ta gaishe da alhaji sannan ta gaishe dasu yaya shahid Husna ta gaisheta hudah tace alhaji yau ni xanyi saving din kowa alhaji yace da kyau hudahna kowa yayi farinciki da sauya warta ta saki jiki tana walwalarta kuma suna mamakin sauya warta haka suka ci abinci suna hirarsu gunin shaawa ita Kanta hudah bata san meke faruwa da ita ba saboda yau tunda ta tashi takejin farin ciki ko don xataga abin kaunarta ne sir Haidar oho suna gama karyawa kowa ya tashi hajiya tace in sameta a daki falo ya rage daga hudah sai yaya jadeed hudah tace yaya yau naga kowa sai farin ciki yakeyi a gidan meyasa jadeed yace saboda mun ganki cikin farinciki hudah tace lallai yaya kuna so inyi farinciki xakuyi min auren dole uhm jadeed yace hudah ki daina wannan maganar muna sonki muna son farincikinki kiyi hakuri ki dauki auren nan a matsayin kaddararki Husna sako tace aunty hudah hajiya na kiranki hudah tace to ta tashi ta tafi dakin hajiya ta sameta a xaune tana duba wani Littafi hudah tayi sallam ta shiga wuri ta samu ta xauna
Hajiya ta dago ta kalli yar tata tace maganinki xaki sha hudah ta bata rai tace hajiya ni baxan sha ba saida hajiya tayi da gaske sannan tasha hajiya tace gobe mai dilka xataxo saiki shirya hudah tace hajiya gobe xanje skull fa hajiya tace ai keda makaranta kuma sai dai bayan aurenku idan ya yarda sai ki cigaba hudah ta rushe da kuka tace hajiya ya xakuyi mun haka don Allah ku fada masa ya barni in cigaba da karatuna hajiya tace kiyi shiru ki share hawayenki insha Allah xai barki jin haka yasa xuciyarta yai Sanyi ta goge fuskarta tace Allah ya yarda hajiya ta amsa da ameen
Hudah tace hajiya bari inje wurin jiddah hajiya tace adawo lafiya dakinta ta koma ta dauki wayarta da mayafinta sai gidansu Jidda a falo ta tarar da Abbu da ummi ta tsugunna ta gaishe su sannan ta wuce dakin Jidda bata dakin gefen gado ta xauna tajiyo karar ruwa a toilet alamun tana wanka agogo ta kalla karfe goma da rabi na safe bata ida kallon agogon ba wayar dake hannunta ya soma kara ta duba fuskar wayar sir Haidar ne daga wayar tayi tare da yin sallama gaisawa sukayi ya shaida mata yana fitowa 11am idan ya shigo xai kirata
Jidda ce ta fito daga wanka tace kai hudah iriin wannan kwalliya haka ga kamshi da kike xubawa duk dakin ya gauraye da kamshi duk dai saboda sir Haidar ne hudah tayi tsaki mtsww tace ke wlh kin cika fassara to wannan tsinannen kamshi da kikaji inayi to wani turare ne hajiya ta bani wai in rika sawa a ruwan wanka da kuma wasu shegun magungunar da aketa bani ni banga dalili ba Jidda tayi shewa tace Amarya kin sha kamshi kice gara in fara lallabaki tun yanxu kona samu tabarraki hudah tayi tsaki mtsww tace dalla malam kiyi sauri ki shirya ya kusa xuwa Jidda tace to wai tsaya a ina xaa sauke shi hudah tace anan gidan mana Jidda tace kin san yaya Dalhat na nanfa kada ya ganshi yayi masa wulakanci kin san dai halinsa hudah tace insha Allah ba xai ganshi ba can garden xamu xauna Jidda xatayi magana kenan wayar hudah ya soma ringing ta daga wayar yace gani a waje naga gida iri daya guda biyu wanne xan shiga
Hudah tace ka daga Kanka sama xakaga hoton flower daya green daya red sai ka shigo inda kaga green yace gashi nan shigowa fitowar mu yayi daidai da shigowarsa farfajiyar gidan so ba bata lokaci ya fito hanyar garden muka bi yana biye damu har muka isa wurin xama katon kafet ne shimfide a kasa.....
π±π±π±π±
muffy
π±π±π±π±
π°π°π°π°π°
AUREN DOLE
π°π°π°π°π°
bismillahir rahmani raheem
Story
And
Written
by
mufeeda Muazu
Page 91to100
Salam masoya littafin auren dole ina mai baku hkr a bisa shirun da kukaji wannan ya farune saboda ayyukan da sukayi min yawwa but yanxu komi yayi dai dai ngd
Har garden hudah ta kaishi katon kafet ne shimfede a kan kafet grass din dake wurin Hudah tace mishi bismillah ka xauna ta fada tare da xama sir yayi murmushi ya xauna Jidda da Hudah suka gaishe shi a tare amsawa yayi cike da faraa shimfide a fuskarsa daga ganinsa kasan yana cikin farin ciki ganin haka hudah tace Allah sarki gsky ina tausaya mana cikin xuciya take wannan maganar sunyi shiru na dan wani lokaci jiddah ce tace bari in kawo ma babban bakon namu ruwa hudah tace yi sauri Jidda wlh sam na manta Jidda tace ai dole ki manta saboda farin ciki hudah ta harareta tace dallah kiyi sauri kada ya gaji da jira Jidda ta tafi tana dariya sir Haidar yayi murmushi yace hudah kuna burgeni keda yar uwanki uhm kawai hudah tace sir Haidar yace hudah yau gani a gidanku fatan xaki karbe ni hannu biyu hudah tayi murmushi dai dai lokacin Husna taxo da sallama tare da aje tray a kusa da sir Haidar ta tsugunna ta gaisheshi ya amsa cike da faraa hudah tace Husna ina Jiddan take Husna tace tana can yaya Dalhat ya kirata hudah ta xaro ido π tace dama bai tafi ba Husna tace eh hudah tace shikenan jeki Husna ta tashi tafi hudah ta juyo wurin sir Haidar tare da yin murmushi tace dan Allah kayi hakuri sir haidar yace ah bkm ai ruwa lemu da snacks ne a tray din da Husna ta aje hudah ta xuba masa ruwa da lemu a Kofi ta aje masa yace to ngd da kulawa sir Haidar yace Husna Kanwar mu ce ko don naga kuna kama sosai kaman an tsaga kara hudah tace eh itace auta sir Haidar yace da kyau tare da aje kofin lemu
jiddah kuwa tunda ta fito da tray xata kawo Dalhat ya tsareta wai ina xata kai kuma motar waye a compound Jidda ta rude saiga Husna tamika mata tray din tace takai garden Dalhat ya dakawa Jidda tsawa yace bada ke nakeyi ba motar wanene wato ke kin kawo kai aure kike so ko har kin fara kawo samari ko ya rike hannunta xai fara janta tace yaya Allah ba bakona bane wurin hudah yaxo sakinta yace hudah lallai xata gane kurenta dan ina ne don nasan bakinku daya da ita Jidda tace don Allah yaya kayi hakuri wlh ba soyayya sukeyi ba wani mugun kallo ya watsa mata hakan yasa taja bakinta ta tsuke fita yayi daga falon su hudah kuwa tana garden ana hira da sir haidar jefi jefi saboda rashin sabo hudah taga shirun yayi yawa ne yasa tace bari duba tagan ta mike kenan sai ga Jiddan komawa tayi ta xauna Jidda tace don Allah kuyi hakuri aikine ya tsareni sir Haidar yace ah bkm ranki ya dade sunyi shiru na dan time Jidda tace sir muna mai baka hakuri abinda xamu fada maka ba daga mu bane haka Allah ya tsara sir haidar yace to ina jinku Jidda ta xayyane masa duk abinda ke faruwa game da hudah akan auren da xaa yi mata daga karshe tace dan Allah yayi hakuri sun xabi su fada masa gaskiya ne saboda hudah na sonka sosai shiyasa hudah dake gefe tuni hawaye ya wanke mata fuska sir Haidar kuwa jikinsa duk yayi sanyi ya dukar da kai shiru ya ratsa na tsawon 5min sir Haidar ne yayi karfin halin dagowa idonsa ya kada yayi ja yaga hudah na xubar kwallah yace bkm Jidda na fahimce ku kuma ngd da baku rufeni ba Allah ya saka da alkhairi hudah kiyi hakuri haka Allah ya kaddara insh Allah xamu cigaba da xamunci a karshe kuma ina rokon alfarma a gurinku Jidda tace toh Allah yasa baxai gagare mu ba sir haidar yace baxai gagara ba insha Allah
Idan ba damuwa Husna nikeso a bani nidai ina son jininku don Allah ku taimaka mun hudah ta goge fuska tace insha Allah xanyi kokari but ka nemi soyayyarta sir Haidar yayi godiya tare da aje musu kudi mai yawa yace suyi hakuri dashi bayawa sunyi sunyi ya barshi yaki hakanan sukayi masa godiya har wurin motarsa maigadi ya bude masa gate ya tafi haka suka rabu cike da damuwa.......
π±π±π±π±π±
muffy
π±π±π±π±π±
For comment 07065642314
π°π°π°π°π°
AUREN DOLE
π°π°π°π°π°
Bismillahir rahmani raheem
Story
And
Written
by
mufeeda Muazu
Page 101. 105
Dedicated dis page 2 my cwt sis First LadyπΉ
Yana fita daga gate din Jidda da hudah suka juya cikin gidan cike da damuwa ashe duk abinda sukeyi Dalhat yana hangensu ta window suna komawa ciki kuwa ya fito ya bisu koda suka shiga bakowa a falo xama sukayi hudah ta dauki remote ta kunna tv ko xataji saukin xugin da xuciyarta keyi minti kadan sukaji an bugo kofa da karfi dago Kan da xasuyi ne suka hada ido Dalhat cikin daurewar fuska ya kariso har inda hudah ke xaune kirjinta sai dukan tara tara yakeyi jikinta harya fara rawa Fada Fada ya soma magana waye yaxo gurinki hudah tai shiru batace komi ba tsawa ya daka mata bada ke nakeyi ba hudah ta dago Kanta hawaye ya wanke mata fuska tace lecturer din mune Dalhat yace oohh dama abinda kukeyi kenan an tura ku karatu kuna soyayya jidda tace Allah yaya ba soyayya mukeyi ba Dalhat yace rufemun baki kafin fasa shi Jidda taja bakinta tayi shiru ya dawo Kan hudah yace dukda ba sonki nikeyi ba baxan dauki shashanci ba wlh na kuma ganinki da wani ranki xai baci
Hudah ta goge kwallar daya xubo mata tace da kake cewa baka sona nima ai ba sonka nikeyi ba kuma duk wanda yace yana sona sai na kulashi mari ya kai mata jikake tass rike wurin tayi ta dago xa tai magana ya kara mata a dayan kuncin sai data ga wani haske kamar wuta ta fashe da kuka ta tashi ta nufi hanyar fita Jidda ta tashi xata bita Dalhat ya hanata hakanan ta koma ta xauna badon ranta yaso ba hudah kuwa tana fita compound din gidan idonta yakai wurin wani katon karfe da gudu taje ta dauki karfen tana waigowa ta ganshi ya kofa ya harde hannun a kirji yana kallon ikon Allah dai dai time data juya da gudu dai dai ummi da yaya shaheed suka shigo gidan da sauri yaya shahida ya bi bayan hudah ita kuma ganin yaya shahid ya biyota ta kara da gudu
Shima ya kara da gudu ummi kuwa sai xabga salati takeyi tana kiran hudah ita kuma hudah ina hankalinta ya tafi tana xuwa ta daga karfen ne yaya shahid ya rike yana kokarin kwacewa amma ina ya kasa yaya Dalhat yace barta kawai mara kunyar karya kawai shima yayi ya kasa kowa na mamakin irin karfi haka itako hudah ba abinda take sai kuka taki kula kowa duk cikansu sun rasa yadda xasuyi da ita ummi ta hau fada wai me yaya Dalhat yayi mata haka ta inda take shiga batanan take fita ba jiddah tace ummi anya huda ba aljannu ne da ita ba sai a lokacin hudah ta bude ido tace kalau nike banida komi yaya shahid yace saki karfen nan hudah tace baxa saki ba mari a dauketa dashi ba shiri ta saki taje ta rungume ummi tana kuka tace ummi wlh yaya Dalhat bai sona Allah idan aka daura auren nan kasheni xaiyi hawaye duk ya bata mata fuska ummi ta goge mata fuska sannan tace shahid ku biyoni falo ta rike hannun hudah suka shiga kowa ya xauna shiru falon yayi baka jin komi sai shasshekar kukan hudah
Ummi ta fara magana cikin bacin rai tace shahid da kai Dalhat duk wanda ya kuskura ya kara taba hudah wlh sai ranshi ya baci kun girma baku san kun girma ba Dalhat yace ummi wlh duk ke kikesa su raina mu ummi tace yi ma mutane shiru ku tashi Ku bani wuri hudah tai musu gwalo sunji haushi amma ba yadda suka iya haka nan suka fice ummi tayita lallashin hudah hartai shiru sai dai fuskanta sun kumbura tace ummi xan tapi gida jiddah ta taso suka fita tare a gate suka hadu da yaya Dalhat ya taresu yace ke bar ganin kina gaban ummi wlh kika shigo hannuna sai kin gane kurenki ke kuma Jidda bari alhaji ya dawo kema aure xa ai miki kowa ya huta marasa kunyar yara kawai......
π±π±π±π±π±
muffy
π±π±π±π±π±
For comment 07065642314.
π°π°π°π°π°
AUREN DOLE
π°π°π°π°π°
Bismillahir rahmani raheem
Story
And
Written
by
mufeeda Muazu
Page 106 .110
Dedicated dis page to my friend classic Feedoh
Wucewa sukayi ba wanda yace masa komi shiko gida ya koma ya hada kayansa xai koma wurin aiki dama ya sa ba tafiyar dare yana gama hada kayansa ya fito ya nufi dakin ummi ya durkusa har kasa yace ummi yau insha Allah xan koma wurin aiki ba yabo ba fallasa tace Allah ya tsare Dalhat yace Ameen sannan tace ina fatan ka sallami amarya da kawayenta yace aa ummi sai nadawo ranar alhamis kuma ma ai basuce suna bukatar wani abuba ummi ta bata fuska tace ooo sai sun tambaya tayi kwafa Dalhat yace kiyi hakuri ummi bari inje banki in dawo bata daice komi ba harya fita yana fita yaci karo da Abbu a waje ya duka ya gaishe shi Abbu yace Dalhat wai yaushe xaka koma ne Dalhat yace yau insha Allah Abbu yace amma shine har yanxu baka fara shiri ba kafiso kayi tafiyar dare ko Dalhat ya sosa keya yace na shirya ummi ce tace wai sai na sallami su Jidda shine xanje banki in dawo sai in tafi
Abbu yace kai wannan ummin taku akwai rigima Dalhat dai murmushi yayi baice komi ba Abbu yace kada ka damu nixan bada Sannan yace umminku tace anan xaku xauna xansa a gyara muku part din can da bakowa Dalhat yace Abbu Don Allah ka rokar mun ita ta barni in tafi da ita xaria kafin in gama gidana Abbu yace kayi hakuri Dalhat kabi maganar mahaifiyarka na dan lokaci kadan ne Dalhat yayi wa mahaifinsa godiya tare da yi masa sallama abbu yayi masa fatan alkhairi Dalhat ya koma ciki ya dauko jakarsa ya saka a mota yaje yayiwa ummi sallama Allah ya tsare kawai tace a sanyaye ya fita gidansu hudah ya shiga yayiwa su hajiya da alhaji sallama cikin kulawa sukai masa Allah ya tsare hanya yaji dadin haka ya fito ya dauki hanyar xaria ankai akwati doxin kaya na gani na Fada gsky kaya sun burge kowa amma banda amarya wanda tunanin irin xaman da xatayi a gidan wanda baya sonta bata sonsa amarya tasha gyara sosai kaman ka taba jini ya fito ga kamshi mai dadi datakeyi
Yau Jumaa kuma yaune xaai walima amarya hudah na kwanace a daki ba abinda take sai kuka Jidda ta shigo dakin ta ganta a cikin wannan hali Jidda taxo ta xauna kusa da ita tace haba Sis don Allah kiyi hakuri ki daina kuka kinga fah ga kawayen mu can da yan skull din mu a falo hadah ta kalleta kallo irina tuhuma tace a iya sani na bamuyi gayya ba Jidda tace eh hajiya ce tace in gayyato su hudah tayi kwafa tace dai dai ne Jidda tace yanxu dai kiyi hakuri ki tashi kiyi wanka ga mai kwalliyi can tana jiranki hudah tace ba wankan da xanyi malama ki tashi ki bani wuri ni na kulama farin ciki kikeyi tayi tsaki ta juya baya Jidda tayi juyin duniya fur huda taki tashi hakanan ta hakura ta tashi ta fita wurin aunty Asiya taje kanwar hajiya ta Fada mata hudah fah ta tubure tace ba xatayi wanka ba gashi lokaci na tafiya aunty Asiya ta fusata dama ita akwaita da fada dakin sukaje yadda Jidda ta barta haka suka sameta Aunty Asiya ta maka mata duka a baya ta juyo da niyyar masifa tayi toxali da aunty Asiya Jidda kuma na bayanta hudah ta bata rai Aunty Asiya tace tashi ki shiga wanka ba damar musu don tasan aunty Asia sarai tashi tayi tana Kunku nai ta shige toilet Jidda kuma taje ta kira mai kwalliya
bata Jima ba ta fito daga wankan aunty Asia na xaune a bakin gado ga Jidda da mai kwalliya kuma Jidda ta mika mata kayan da xata sa toilet ta koma ta saka kayan ta fito tana tura baki mai kwalliya ta tsantsara ma amarya kwalliya na gani na Fada Sannan akayiwa Jidda Dalhat kuwa bai shigo bauchi ba sai bayan sallar jumaa....
π±π±π±π±
muffy
π±π±π±π±
For comment 07065642314
π°π°π°π°π°π°
AUREN DOLE
π°π°π°π°π°π°
bismillahir rahamanir raheem
Page 111- 115
*story nd written by Mufeeda Muazu*
*Dedicated dis page 2 my swt twin Sis Hanifa Muazu Allah ya barmu tareπ*
Amarya kuwa da kyar aka samu ta tsaya akayi mata kwalliya gashi tayi kyau sosai kaman ba ita ba inba wanda ya Santa sosai ba baxaka ganeta Dalhat kuwa yana shiga part dinsa ya nufa saboda cika da gidan yayi wanka ya farayi ya dan kwanta don ya huta bai San time din da barci ya dauke shi ba bashi ya tashi ba sai karfe shidda na yamma lokacin ne kuma amarya da kawayenta suka dawo daga wurin walima hudah na tsaye ita da wani course mate dinsu da yaxo tayasu murna shida abokinsa Jidda da kawayensu kuwa gida suka shige hudah ta gaishe su Adam yace amarya kawai sai mukaji lbrn aurenki gaskiya munji mamaki saboda yadda mukaga bakya kula kowa a skull duk da irin tarin masoyan da kike dashi shiko waye wannan mai saar murmushi hudah tayi dagowar da xatayi suka hada ido da Dalhat ya harde hannayensa Kana nan kayane a jikinsa fuskar nan murki kawar da kanta tayi suka cigaba da hiransu basuyi aune kawai sai ganin mutum sukayi a gabansu Adam ya mika masa hannu Dalhat ya maida hannu fuskar nan a daure
Ya fisgota da karfi yana Janta tana tirjewa cikin gida ya shige da ita part dinsa ya rufe da key yasa key din a aljihu hudah kuwa ta cika tayi dama jira takeyi kawai ta fashe idonta ta dago ta kalleshi tace dallah malam ka budewa mutane kofa niba yar iska bace da xaka kawoni daki ka kulle murmushi yayi ya matso kusa da ita har suna iya jiyo numfashin juna Dalhat yace ke ba yar iska bace sai wane hudah tai shiru Kanta a kasa tsawa ya daka mata har saida yan hanjin cikinta suka kada tuni hawaye suka wanke mata fuska ya cigaba da cewa suwaye naganki dasu a waje bayan kinsan ke matar wani ce wannan shine iskanci kuma wlh duo randa kika shigo hannuna xaki gane kurenki duk da kince kashina bai gama kwari ba hudah dai shiru tayi bata kara cewa komi ba har ya gama sai dai idonta ya kada yayi jawur kaman jar gauta saboda bacin rai wannan shine a dake ka a hanaka kuka
A can gida kuwa Jidda taji hudah shiru ta fito waje bataga kowa ba gashi magriba ta kusa kawayensu har sun gaji da jira Jidda ne ta sallamesu jiddah na xaune tayi jigum tana tunanin ta ina hudah xata bullo Safiyyah ce ta shigo dakin yar wan hajiya ce saar su hudah ne tace Jidda wai ina amarya ne su mama na nemanta Jidda tace wlh tunda muka dawo daga wurin walima ta tsaya suna gaisawa da maxan class dinmu najita shiru koda na leka ban ganta ba Safiyyah tace toh fah to kinkira wayarta Jidda tace aa bari in kirata ta dauki wayarta tayi dialing no yaki shiga har suka gaji da kira Jidda tace mun shiga uku Allah yasa dai ba guduwa tayi ba Safiyyah tace haba dai mu shiga gidanku mana mu gani ko tana can Jidda tace anya kuwa Safiyyah tace mudai duba Jidda tace to muje hudah kuwa yana bude kofa ta fito a guje tana sauri ta koma kada wani ya ganta jitayi an rike hannunta Aunty hanifa ce tace amarya daga ina haka hudah dai bata ce komai ba Aunty hanifa tace xo mushiga ciki tunda baxakiyi magana ba hudah tace ni gidan mu xan tafi hanifa tace banda abinki da nan da chan ai duk dayane to muje can din a gate suka hadu dasu Safiyyah Jidda tace ina kika shiga ne tun daxu aketa nemanki hudah tace ina ruwanku ni ku kyaleni Aunty hanifa tace ku kyaleta don Allah ta huta Safiyyah tace Jidda kyaleta kawai ana so ana kaiwa kasuwa hudah ta Dada jin haushi ta bisu da gudu suka shiga gidan Safiyyah daga nesa tace idan kin gama kumburen2 su mama na nemanki a daki Safiyyah tayi mata gwalo π ta shige abinta hudah tace Aunty hanifa kin gansu ko hanifa tace kyalesu kawai xanyi maganinsu.......
?
muffy
π±π±π±π±
π°π°π°π°π°π°
[5/23, 08:23] Umar Dalha: π°π°π°π°π°π°
AUREN DOLE
π°π°π°π°π°π°
bismillahir rahmanir raheem
Story
And
Written by
Mufeeda Muazu
Page 116. 120
Wannan shafi sΓ daukarwa ce ga mosaya Littafin Auren dole ina ganin sakonninku ngd Allah ya bar xumunci Ameen
Asabar
A yau ne dubban mutane suka shaida auren Hudah Abubakar Sadiq da angonta Dalhat Aliyu yayinda daurin auren ya samu tarin manya kuso shin gwamnati na Nigeria iyayen amarya da ango sai murna suke Sabanin amarya da ango wanda shi Dalhat ya dake ba kowa bane xai fahimci halinda yake ciki sai wanda ya Sani ita ko amarya tunda taji an daura auren take ta kuka su Jidda nata lallashinta amma fir taki yin shiru sumayya tace Jidda ki kyaleta kukan dadi takeyi yau xata gidan mijinta sauran yan uwansu da suke dakin suka hau shewa Hudah ta kara kulewa ta tashi tsaye kwance daurin Kanta tayi ta jefar da dankwalin ta dauki gyalenta xata fita jidda ta riko hannunta tace meye haka hudah yanxu abinda kikeyi kinga ya dace kenan haba aure dai an daura babu abinda ya dace kiyi sai fatan samun xaman lpy muma yan uwanki xamu tayaki insha Allah sumayya ta matso kusa da ita tana share mata hawaye tace kiyi hakuri hudah kinga duk kin bata kwalliyarki ki daure insha Allah komi xai xama tarihi amma fah sai kinyi hakuri
Hudah dai tai shiru bata kara cewa komi ba ita kadai tasan irin xugin dayake mata ta daina kuka da hawaye sai kukan xuci a bangaren Dalhat kuwa ya sake sai hira yake da abokansa suna tsokanarsa shi kuma yana biye musu da ya gaji tashi yayi ya shige daki abinsa wayarsa ya ciro daga aljihu yayi dialing no hudah kawai sai yaji karar wayar a dakin tashi yayi ya dauko wayar ga sunansa nan a Kan wayar an rubuta yaya Dalhat bai san time din da yayi murmushi ba ni mufeeda danake gefe nace wannan murmushi na meye oho tunani yake ya akayi wayarta ta shigo dakinsa sai ya tuna Ashe fah jiya ta shigo layin Jidda ya kira har ya katse bata daga ba sai a kira na biyu sannan ta daga shima sai daya kusa katsewa Fada ya fara yi mata wai don mene take kiranta baxata daga ba hakuri ta bashi tace bata kusa ne gyara kwanciya yayi Sannan yace ina hudah jiddah ta kalli hudah dake kwance idonta a lumshe Dalhat yace bakiji menace bane halan Jidda tace bata kusa bari akai mata
Katse wayar tayi taxo ta kamo hannun hudah tace xo muje kiji tayi haka ne Saboda kawayensu sake dakin don tasan hudah xata iya basu kunya ita dai hudah xama kamar gunki Jidda sai janta takeyi har ta Samu wurin da ba mutane sannan suka tsaya wayar ta fara kuka Jidda tai sauri ta daga tace gata nan ta mika ma hudah wayar hudah tace wayene Jidda tace kisa a kunnenki mana sai kiji hudah tace wlh sai dai insa a handsfree jidda tace oho dai ke kika Sani duk abinda suke Fada yana jiyo su karban wayar tayi tasa a handsfree Sannan tace hello waye Dalhat dake kwance tashi yayi ya xauna yace mijinki ne Dalhat jin sunansa sai da gabanta ya fadi ta kalli Jidda dake gefe itama ita take kallo ya cigaba da cewa alhmdllh yau an daura aure kuma insha Allah yau ba sai gobe ba xaki banbamce kashina yayi kwari ko baiyi ba kuma xan gwada miki iskanci na kinsa a handsfree ko to duk cikin wadanda sukaji ba mai cetonki don haka sai ki fara shiri xuwa anjima
Yana gama fadar haka ya katse wayar hudah ta dago da jajayen idonta da suka rine Saboda kuka gashi muryarta ya dishe tace Jidda Kinji ko kinji abinda yaya Dalhat yace ko toh wlh ba xan iya ba muje ki fadawa su hajiya kada su kaini gidansa kasheni xaiyi ta fashe da kuka mai tsuma xuciya Jidda tace kiyi hakuri xancen fadawa su hajiya bai taso ba hudah tace to ni yanxu ya xanyi kin dai ji muguntar daya shirya Jidda tace eh mafita dayace kiyi hakuri duk abinda ya saki kada kiyi masa musu ko gardama ina ganin hakane kawai mafita hudah ta mike tsaye tace haba hudah wannan ba mafita bane
π±π±π±π±
muffy
π±π±π±π±
[5/23, 08:24] Umar Dalha: π°π°π°π°π°π°
AUREN.DOLE
π°π°π°π°π°π°
bismillahir rahmanir raheem
*story and written by mufeeda Muazu*
*Page 121.125*
*Dedicated this page 2 my cousins Sisters salmerh nd Hafsat Nasir Allah ya bar xumunci*
Jidda ta mike ta matso kusa da hudah ta dafa kafadarta tace yanxu meye mafita tunda kince shawarar dana kawo baiyi ba hudah taja dogon numfashi tare da xubda kwallah tace jidda nidai taimako daya xakiyi mun jidda tace wani irin taimako hudah tace yawwa so nake don Allah idan an Kaini gidanku ku xauna a dakin kasa kada don Allah kada ki rufe kofar baya Jidda tace me hakan ke nufi hudah tace hakan yana nufin idan an kaini kowa ya watse xan gudo wurinku kinga ba.kowa a kasa asirin mu a rufe koda ya shigo sai dai yaga bakowa jidda tace haba hudah kin Sani dai komi gudun da xakiyi sai ya kusanceki tunda dai an riga an daura aure to meya yi saura gara kiyi hakuri kawai nan da wata tara mu sha suna ta karshe maganar cikin tsigar tsokana hudah tace wlh jikina bana Dalhat bane bai isa ba jidda tace to shikenan xanyi yadda kika ce tunda kinki jin shawarata komawa cikin daki sukayi ita dai hudah jikin ta duk yayi sanyi
Dalhat kuwa tunda suka gama waya da hudah ya Fada kogin tunani wani sashi na xuciyarsa tana cewa kada yayi mata abinda yayi niyya wani sashi kuma tana ingixa shi yana cikin tunanin ne yaji kiran sallar magriba firgigit ya tashi kamar ya tashi daga barci falo yafito ya tarar da abokanansa sun fita waje suna alola shima daki ya koma yayo nashi alolar a kofar masallaci ya same su shiga sukayi
Amarya kuwa tunda taga yamma tayi take kuka su Jidda sunyi lallashin har sun gaji bayan sallar issha ne Aunty Asiaya ce ta shigo dakin ta tarar da hudah can karshen gado tana kwance a lokacin kawayensu duk san tafi ya rage saura su sumayya Aunty Asia ta xo kusa da ita tace hudah ki tashi ki shirya yanxu xaa kaiki dakin mijinki hudah ta dago kai ido cike da kwallah tace aunty niba inda xani dan Allah ku kyaleni kin San meya ce mun aunty Asia tace aa sai kin fada ta bude baki xatayi magana Jidda tai sauri ta toshe mata baki tace aunty shirmenta ne kawai yanxu xata shirya aunty Asia tace to shikenan na baku nanda 10mins tana gama fadar haka ta fice a dakin
Tana fita sumayya suka tasata saida ta canja kaya lass tasa red da ratsin fari a jikinsa Sadiya ce tayi mata daurin dan kwali Sannan Jidda ta miko mata gyale white takalmi shima white xama tayi a gefen gado tana hawaye ba wanda ya sake magana dakin yayi shiru aunty binta ce tashigo maman sumayya koda tashigo ta tarar da amarya ta shirya tsaf tace yawwa Ashe kin shirya hudah dai batace komai ba sai kwallah daya taru mata a ido Aunty Binta rike hannunta tayi tace muje jiran mu akeyi fita sukayi a dakin su Jidda suka mara musu baya alhaji ya fita a gidan ne don yasan da kuka xasu rabu wurin hajiya aka kaita tayi mata nasiha hajiya cewa tayi abinda xatace saboda abinda xatace sun riga sun fada don haka addua tayi musu Allah ya bada xama lpy suka amsa ameen hudah kuwa sai kuka take da kyar aunty Asia ta dagata suna fitowa farfajiyar gidan motoci suka gani jere Kanwar alhaji Goggo Umma tace wai baga gidan da xaa kaita ba meye na kawo wasu motoci kuma shahid dake tsaye yace Goggo xaa dan xagayo ne ba yadda ta iya dole ta hakura ya nuna musu motar da amarya xata shiga Jidda ce a gaba baya kuma amarya a tsakiya gefen dama Aunty Binta gefen hagu kuma Goggo Umma shaheed ne ke tuka motar motoci shidda ne reras suka jero mai gadi ya wangale musu gate sai da sukayi xagayensu sannan aka kai amarya gidanta side din ummi aka fara xuwa da ita suka damka amana ummi da yan uwanta sun amshesu hannu biyu godiya sukayi Sannan suka wuce da ita part dinta...........
muffy
π±π±π±π±π±
For comment 07065642314
*AUREN DOLE*
π°π°π°π°π°π°
*Tπ °LENTED WRITERS FORUM*
❄❄ *T•W•F* ❄❄
bismillahir rahamanir raheem
Page 126- 130
*story nd written by Mufeeda Muazu*
*wannan shafi nakune yan uwa rabin jiki*
Nafisa Muazu
Aishatu Muazu
Mufeeda Muazu
Hanifa Muazu
Khairat Muazu
Naja'atu Muazu
Ahmad Tijjani Muazu
Abubakar Buba Muazu
Sai dan auta Haidar Aliyu Muazu
Allah ya dada hada Kanmu ya barmu tare love u allππ
Part one last episode
Part dinta aka wuce da ita fuskanta lullube da mayafi har bedroom suka kaita kan gado Goggo Umma ne ta fito ta xageye part din falo biyu ne bedroom ma haka sai kitchen da store falon ta dawo ta Kare musu kallo lallai naira tayi kuka Fadar yadda gidan ya tsaruma kauyanci ne Aunty Binta da Aunty Asia tasa hadah sukayi a gaba sai nasiha suke mata tayi hakuri tabi mijinta tunda dai aure an riga an daura yadda hudah ta nutsu tana saurarensu a sha ta dauki nasihar da sukeyi mata basu San shiga yakeyi yana fita ba ita kadai tasan abubuwan da take kullawa a ranta Aunty Asia ta dauko Jakarta ta bude ta ciro madara peak da wani magani ta dauko Kofi ta hada sannan ta mikawa hudah da Kanta ke lullube tun shigowarsu da kyar ta amsa tana ya mutsa fuskarta tace aunty meye wannan kuma ni gaskiya baxan sha ba nagaji da dure duren da kuke min aunty binta tace ehe lallai wuyarki yayi kauri xaki shanye ki bani kofin ko sai na Saba miki ganin ba wasa a idonta yasa ta kafa kofi a baki sai da ta shanye ta aje Kofin
Aunty Binta tace yawwa hudah ko kefa a tare suka mike itama hudah mikewa tayi tace aunty yanxu tafiya xakuyi ku barni idonta taf da hawaye hakuri suka bata da kyar ta hakura ta koma a falo suka tarar da Goggo Umma xaune abinta ganinsu ne yasa ta mike tace har Kun fito ne ehe suka ce tace to bari inyi sallama da amaryar sai mutafi aunty Asia tace barta kawai kixo mutafi don wannan amaryar yar daru ce ta leka dayan dakin dasu sumayya suke tace kunxo nan sai xuba kuke maryam tace ai anan xamu kwana mom aunty Asia tace
ba wanda xai kwana ana siyan baki duk ku dawo gida sumayya tace a part dinsu Jidda take nufi ba nan ba aunty tace to wai ina Jiddan take ban ganta ba maryam tace tana waje ita da yaya shahid aunty Asia taja musu kunne sannan tayi musu sai da safe ta koma falo suka tafi
A waje kuwa Jidda ce da shaheed sai hirar sukeyi cikin kwanciyar hankali shaheed yace swthrt gsky xanje in samu alhaji inyi masa magana Jidda tace yaya shaheed ba yanxu ka bari a dan kwana biyu mana lokacin kowa ya natsa shaheed yace lallai Jidda ba kya sona kamar yadda nike sonki Jidda tace yaya ba haka bane kawai dai....shahid ya katseta da cewa kawai dai mene ki shiga gida kawai sai da safe xamuyi waya Jidda xatayi magana shahid yace aa jidda gud nyt ya tafi ita kuma jiki a mace ta shige part din hudah ta tarar dasu maryam sai hirarsu sukeyi hudah kuma ta xaune ta xabga tagumi sai kallon kowa take dai dai Jidda tace amaryar mu yadai hudah ta harareta tace dole kice yadai tun daxu kin makalewa juna wai ku ga romio da Juliet ko sumayya tace ah kinga laifinta gara suyi lokacinsu ne ke kitsaya wasa wai bakyaso ko Jidda tace yawwa Fada mata dai sumayya ta kalli agogo karfe 9.59pm tace gaskiya ni bacci nikeji idan ba xasu bane Jidda muje mu kwanta
bata ida rufe baki ba suka juyo sallamar ango da abokanansa Jidda dake kusa da hudah tai sauri ta rufe mata fuska da mayafinta shigowa sukayi ango sai washe hakora kaman da gaske yayi haka ne Saboda abokansa dariyar bai kai xuci haka dai akayi siyen baki suka Dalhat ya tafi rakasu hudah tace Jidda pls kada ki manta da plan din mu Jidda tace kedai bakya jin magana hudah tace ina ruwanki Jidda tace shikenan sumayya tace wlh kudai munafukai ne tun daxu nake ganin Kuna kus kus hudah tace eh din ina ruwanki Jidda tace Ku tashi mutafi Kunji kada ya dawo ya Kore mu da bulala a tare suka mike maryam tace to amarya sai munxo gashi hadah ta tashi da sauri tace uban wa xaku gasa a guje suka fita binsu tayi Dalhat ya dawo daga rakiyar abokansa kenan ya hangosu a xuciyarsa yace har yanxu da kuruciya a tare dasu ganin hudah ta fito da sauri ya karisa ji kawai tayi an rike hannun juyowar da xatayi sukai ido Hudu da Dalhat....
Alhamdulil nan nakawo karshen wannan Littafi na auren dole part Saboda gabatowan watan ramadan wata mai albarka ina fatan Allah yasa mushiga muna masu imani Ameen
Sai bayan sallah in Allah ya kaimu da rai da lpy xukujini a auren dole part 2 insha Allah
masoyana ina godiya da kulawarku gareni love u allπ
baxan manta da alkhairinki gareni ba
First LadyπΉ
Ina godiya Allah ya bar kauna
Ameen
Ramadan Kareem to all muslim ummah
π±π±π±
muffy
π±π±π±π±
Complied by Princess Aysha Muhammad (Humaira)
No comments:
Post a Comment